Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta’addan da FG ke nema ido rufe; Hotuna

1
653

Masarautar ‘Yandoton Daji ta karamar hukumar Tsafe ta yi wa riƙaƙƙen ‘dan ta’adda da gwamnatin tarayya ke nema ido rufe, sarauta.

Taron naɗin sarautar

Ado Aliero, fitaccen ‘dan ta’adda ya samu sarautar Sarkin Fulani daga sabuwar masarautar Sarki Mai Martaba Aliyu Marafa.

Rundunar ‘yan sanda ta taɓa saka ladar N5 miliyan ga duk wanda ya kai Aliero hannun hukumar sakamakon yadda ya addabi yankin Zamfara da Katsina

‘Yandoton daji tana daya daga cikin sabbin masarautu biyun da gwamnatin jihar Zamfara ta ƙirkiro a watan Mayun da ya gabata.

Yadda jama’a suka halarta

An ƙirkiro ta ne daga masarautar Tsafe. Sabon sarkin Yandoton Daji shine Aliyu Marafa. Hukuncin bai wa shugaban ‘yan bindigan sarauta ya biyo baya ne sakamakon ƙoƙarin da yayi na tabbatar da zaman lafiya tare da jagorantar yarjejeniya tsakanin masarautar da ‘yan ta’addan da suka addabi karamar hukumar Tsafe.

An yi nadin sarautar a fadar masarauta Yandoton Daji kuma shugaban masarautar karamar hukumar Tsafe, da kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida, DIG Ibrahim Mamman Tsafe duk sun samu halarta.

Shugaban ‘yan bindigan shi ne ya jagoranci farmakin da aka kai Kadisau, wani yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina inda aka halaka kusan mutum 52.

1 COMMENT

Leave a Reply