DARA TA CI GIDA: Mai safarar mutane ya kashe abokiyar aikinsa, tare da sayarda sassan jikinta

0
202

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Wani magidanci, Dauda Bello kuma shahararren mai safarar mutane, mai shekaru 50 a duniya, ya kashe wata mata ‘yar shekara 71, Messi Adisa tare da sayar Da Sassan Jikinta ga masu harkar tsafi.

“Abokiyar aikina ce a harkar fataucin yara kafin na kashe ta.” Ya shaida wa ‘yan sanda.

Jaridar P.M.EXPRESS ta rawaito cewa jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ne suka yi nasarar kama wanda ake zargin mai suna Bello, inda aka kama shi dumu-dumu da laifin kashe marigayiya Messi Adisa, sannan ya sayar da wuya da idon sawunta ga wani matsafi, kafin bisani ya binne ta a asirce cikin wani kabari mara zurfi.

Sai dai bayan aikata wannan ɗanyan aikin, an kama shi kuma ya amsa laifin ake zarginsa da aikatawa, mummunan laifi da ke kai ga yiwa mutum hukuncin rai da rai a gidan kaso.

Jami’in hulda da jami’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya tabbatar da hakan, ya bayyana cewa wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda ana yi masa tambayoyi tare da tsaurara bincike kan ayyukan ta’addancin da suka yi.

Da ake zantawa da shi, DSP Abimbola ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Alhamis din da ta gabata.

DSP Abimbola ya bayyana cewa: “Bayan ɓacewar wadda aka kashe (dattijuwar), wadda aka gano ta bar gidanta a ranar 8 ga watan Yuni, ba ta dawo ba, hakan ya saka ‘yan uwanta korafi kan wacce ta batan.”

Bayan kama wanda ake zargin kuma ana yi masa tambayoyi, sai ya bayyana cewa ya dade da sanin wanda aka kashen, ya kuma bayyana cewa su biyun dukka ‘yan ƙungiyar harkar safarar yara ne.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa “ya gayyaci wanda abin ya shafa zuwa gidansa ne a ranar kamar kullum, domin su tattauna harkokinsu na safara, amma da isa gidansa ya ga wani abu a tattare da ita wanda yake zargin maƙudan kudade ne.

Sakamakon haka ya bugi matar da sandar katako, domin ya karbi kudin daga hannun ta, wanda hakan ya sa ta suma, nan ya ɗauke ta zuwa daji, karshe ya kasheta ta hanyar.”

Wanda ake zargin ya bayyana cewa bayan ya caje jikin matar Naira  22,200 kawai ya gani, wanda ta karɓa ne matsayin kafin alƙalamin wani aiki. Bayan da ya gane cewa bai samu kudin da ya ke bida ba, sai ya yanke mata wuyan hannu da idon sawunta biyu, ya sayar da su ga wani matsafi domin ya sami ƙarin kudi.

Sai dai wanda ake zargin ya kai ‘yan sanda inda ya binne mamaciyar a wani kabari mara zurfi, an gano gawarta tare da kai ta wajen ajiyar gawa domin daukar rahoton gawar.

Abimbola ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda za ta gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya ta hanyar kama su tare da tuhumar su da laifin hada baki da kisan kai bayan kammala bincike.

Leave a Reply