Gwamnan jihar Zamfara ya tsige Sarkin ‘Yandoton birni kan bama ɗan ta’adda Sarauta

0
261

Gwamnan jihar zamfara ya dakatar da Sarkin Birni ‘YANDOTON , Aliyu Marafa, bisa naɗa sarautan sarkin Fulani ga shahararran dan fashi Adamu Aliero Yankuzo da ake nema ruwa a jallo wanda aka fi sani da Ado Alero.

Matakin da Masarautan ta dauka ya ja ɓacin rai, inda jama’ah ke Allah wadaida irin karramawa da akeyi wa masu laifuka.

READ ALSO: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta’addan da FG ke nema ido rufe; Hotuna

Sai dai a sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya fitar, Gwamnatin na nesanta kanta da matakin da Sarkin ya dauka inda ya dakatar da sarkin tare da kafa kwamitin da zai binciki lamarin.

A halin yanzu, Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shine hakimin Yandoto an nada shi domin kula da Harkin masarauta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here