Yadda Ahmed Musa, captain ɗin Super Eagles, ya rabawa mata da matasa tallafi

1
788

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya bayar da tallafin Naira Miliyan 100 ga zawarawa dubu biyar 5,000 da sauran mata masu karamin karfi a jihar Filato.

Mista Williams Gyang, memba na kungiyar labaran Ahmed Musan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Jos. Gyang ya ce tallafin wani bangare ne na taimakon da Musa yakeyi, da nufin rage wahalhalun da wadanda suka amfana, ke fuskanta.

Ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun raba addinai daban-daban, yana mai cewa yunwa, fatara da miyagu ba su san kabila ko addini ba.

Maryam Abdullahi, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ta godewa dan wasan bisa wannan karamcin da ya nuna, tare da bayyana shi a matsayin wanda Allah ya turo dan ya taimakesu.

Danna wannan alama domin ganin bidiyon Kai tsaye:

Yayin da Ahmed Musa ke raba tallafi ga mata

“Muna fuskantar wahalar ciyar da iyalanmu saboda tsadar rayuwa. “Wannan kudi za su taimaka matuka wajen rage mana radadin da muke ciki da kuma bunkasa kananan sana’o’inmu,” in ji ta.

Musa ya kasance yana aiwatar da irin wadannan ayyukan alheri tun lokacin da ya shahara a matsayinsa na ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa.

1 COMMENT

Leave a Reply