Kotu Ta Haramta Wa Matashi Hawa Doki Na Shekaru 3 A Kano

0
354

Daga; Rabo Haladu.

WATA Kotun Majistare mai lamba 60, ƙarƙashin Mai Shari’a Tijjani Sale Minjibir, ta haramtawa wani matashi hawa doki na tsawon shekara uku.

Matashin, mai suna Abdulsalam Bashir ya gurfana a kotun ne sakamakon ture wata mata da doki har ta samu munanan raunuka.

Bayan hukuncin haramta hawa dokin, alƙalin ya yanke wa matashin, ɗan unguwar Sabuwar Ƙofa da ke a Kano hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya, ko zaɓin biyan tarar naira dubu 25.

Ya kuma umarci mai laifin da ya biya kuɗin magani naira dubu 100 ga matar.

Leave a Reply