An Rufe Wasu Kasuwanni A Jihar Zamfara

0
517

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

GWAMNATIN Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Bello Matawalle, ta bayyana rufe wasu kasuwanni a kananan hukumomi biyu sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro a Jihar.

Kasuwannin da lamarin ya shafa kai tsaye su ne Kasuwannin Mada, Wonaka da Ruwan Bore a karamar hukumar Gusau, da kuma masarautar Yandoto a karamar hukumar Tsafe.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na Jihar Ibrahim Dosara.

Takardar ta ci gaba da bayanin cewa “Gwamna Muhammad Bello Matawalle barden hausa kuma Shatiman Sakkwato, ya kuma bayar da umarnin rufe dukkan kasuwanni da wuraren sayar da Dabbobi a dukkan wadannan yankunan masarautun ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin kuma ta haramta hawan Babura da kuma sayar da Man fetur a Mada, Wonaka da Ruwan Bore da kuma masarautar Yandoto.

“Daga yanzu, dukkan gidajen mai da suke a wadannan wurare duk an rufe su baki daya”.

“Dukkan mutumin da aka samu yana hawan Babur a wanannan wuri za a dauke shi a matsayin dan Ta’adda ne saboda haka an bayar da umarni ga jami’an tsaro su yi harbin bayan da umarni ga jami’an tsaro su yi harbin bayan fage.

Gwamnati ba za ta lamunci a rika cutar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, saboda haka ne aka bayar da umarni ga jami’an tsaro da su hukunta duk wanda aka samu da yin kunnen kashi ga wannan doka kamar dai yadda dokar kasa ta tanadar.

“Kuma Gwannatin ta bayar da umarni ga jami’an tsaron sojoji, Yan Sanda, jami’an tsaron farin kaya da sauran dukkan hukumomin tsaro da su fara aikin magance masu aikata wannan matsala ga tsaro ta hanyar maganinsu a duk inda maboyarsu take.

Leave a Reply