Shugabannin Matasan Arewa Sun Taya Atiku Murna, Sun Sha alwashin Tabbatar Da Ya Ci Zaben Shugaban Kasa A 2023

0
355

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

YAYIN da yake taya mai girma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, gamayyar kungiyoyi sama da 40, kungiyar shugabannin matasan Arewa (NYLF) ta sha alwashin yin aiki domin ganin ya lashe zaben 2023 zabe.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban (NYLF), Kwamared Eliot Afiyo, ya sanya wa hannu wanda aka raba wa manema labarai a ranar Lahadi 29 ga watan Mayu.

Ya ce “ba mu yi mamakin nasarar da Alhaji Atiku Abubakar ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka kammala da sanyin safiyar yau ba, muna farin cikin ganin nasarar da ya samu ta baiwa talakawan Najeriya fatan da suka sha faman a baya-bayan nan domin cikar burinsu.

NYLF, ta ce tana kuma taya jam’iyyar PDP murnar fitar da dan takara mai nasara, wanda zai zama hasken fitila ga ‘yan Najeriya da kuma yankin Arewa da ba ta samu kaso mai kyau na shugabancin kasar a karkashin PDP ba.

“Tare da kammala zaben fidda gwani, (NYLF) nan da nan za ta fara aiwatar da ayyukanta don tattara goyon baya daga tushe ga dan takararmu na zaben shugaban kasa na 2023,” in ji ta.

Kungiyar ta bayyana jin dadin ta da yadda Dattawan Arewa suka shiga tsakani domin ganin Atiku ya samu nasara.

“Muna godiya ga Gwamna Aminu Tambuwal da ya fifita maslahar Arewa sama da duk wata maslaha.

“Muna mika godiyarmu ga kamfanin Teecom a karkashin shugabancin Cif Raymond Dokpesi,” inji su.

Leave a Reply