‘Yan Najeriya Su Tsammaci Kyakkyawan Sakamako Daidai Wannan Lokacin Shekara Mai Zuwa – Atiku Care Foundation

0
268

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

BIYO bayan fitowar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, wata kungiyar jin kai, wato Atiku Care Foundation, ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin samun kyakykyawan sakamako, a daidai wannan lokacin shekara guda kenan mai zuwa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na Atiku Care Foundation, Okpani Jacob Onjewu Dickson, mai kwanan wata 29 ga Mayu, 2022.

“A daidai shekara guda daga yau, ranar 29 ga Mayu, 2023, ya kamata ‘yan Najeriya su sa ido ga sabuwar yarjejeniya, sabon shugaban kasa wanda zai samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

“Mun samu nasara a mataki na daya inda muka samu dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, mataki na biyu kuma zai zama wata nasara da yardar Allah.

“Yan Najeriya za su yi magana da murya daya a rumfunan zabe, zai kasance Atiku ne kuma muna sa ido kan hakan,” in ji sanarwar.

Ya bayyana cewa, tuni babban daraktan gidauniyar, Ambasada Aliyu Bin Abbas ya ba da umarni ga daukacin sassan gidauniyar ta Jahohin da su fara gudanar da gagarumin gangami daga tushe a dukkanin shiyyoyin siyasar kasar nan.

Leave a Reply