Babban Taron PDP: Atiku Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasa

0
319

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya yi nasarar lashe fidda gwani domin samun tikitin Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), domin zama dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Nasarar da za a iya kwatanta ta a matsayin wata babban nasarar da ya yi a babban taron Jam’iyyar ta PDP a garin Abuja, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 371 inda ya doke abokin hamayyarsa na Jihar Rivers Ezenwo Nyesom Wike wanda ya samu kuri’u 237.

Magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar sun kasa dakatar da jin dadinsu lokacin da aka bayyana cewa Atiku ne kan gaba yayin kidayar kuri’u yayin da suke rera taken “Atiku na zuwa.”

Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga takarar tare da goyawa Atiku Abubakar baya kafin a fara zaben.

A jawabinsa bayan tabbatar da nasarar, Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya yabawa kudurin Gwamnonin PDP da kwamitin ayyuka na kasa da wakilai da kuma iyalan PDP bisa jajircewarsu na ganin an samu nasarar babban taron inda ya bayyana shi a matsayin wani tsari na gaskiya da gaskiya da jam’iyyar ta gudanar.

“Yin nasarar gudanar da babban taron shi ne wani ci gaba a cikin tsarin da ake yi na karfafa ribar da muka samu a siyasance,” in ji shi.

Ya yi alkawarin maido da hadin kai tare da baiwa al’ummar kasar damar shiga cikin kasar da ke fama da rarrabuwar kawuna sakamakon rashin jituwa da gwamnatin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta haifar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya kuma bayyana nasarar da ya samu a matsayin wata dama ta sauya wannan hanyar da ta bata.

Atiku Abubakar ya shawarci wadanda basu ji dadin sakamakon ba, da su warware sabanin da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi maimakon su garzaya kotu, yana mai cewa PDP na da tsarin cikin gida na warware rigingimu, inda ya bukace su da su yi amfani da damar da ta samu.

Zaben 2023 zai kasance karo na 6 Atiku Abubakar zai tsaya takarar kujerar shugaban kasar Najeriya mai girma.

Leave a Reply