Shin Allura Za Ta Tono Garma Dalilin Rashin Lafiyar SSA Media Na Gwamna Masari?

0
896

GWAMNA Aminu Bello Masari ko shakka babu yana yin duk abin da ya dace don tafiyar da mulkin jihar Katsina, kuma ya zama rijiya mai ba da ruwa amma guga ta hana, don kuwa kusan haka ake bayyana mafi yawan jami’an gidan gwamnatin jihar da yin kutungwila da kafar ungulu ga tsaftatattun abokan aikin Gwamna Masari.

Wannan batu kamar yadda jama’a da dama suke furtawa wadanda suka nemi a boye sunansu sun ce lallai kam wasu manyan jami’an gwamnatin jihar ta Katsina sun amince su ji kunnyar lahira amma ba ta duniya ba, don haka babu abin da ba sa iya aikatawa.

Bayanansu suka ci gaba da cewa, SSA Media, wato AbdulBasir Labaran Malumfashi bawan Allah ne masoyi ga Gwamna Masari kuma amininsa wanda a harkar jarida ya san aikinsa ba sai an fada ba, amma ya sha fuskantar matsaloli daban-daban daga manyan kurayen nan da ba sa jin tsoron Mahaliccinnsu don kawai neman duniya. Yanzu ga shi mun wayi gari ga mu ga kakakin Gwamna jikinsa a shanye ba ya ko iya furta komai daga bakinsa. Muna fata da rokon Allah SWT da Ya kawoo masa dauki Ya ba shi sauki Ya warkar da shi amin doon rahamaniyarSa.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa ga gidan rediyo DW Hausa, Dokta Ahmad Muhammad Jibiya ya ce, a wasikarsa cewa ko shakka babu Gwamna Masari rijiya ne mai bayar da ruwa don yana bai wa kowane ofis hakkinsa sai dai gugar hanawa take yi, wannan shi ne matsayin jami’an gwamnatin jihar ta Katsina.

Wakilinu ya ce wannan rashin lafiya ta Abdul Labaran Malumfashi cike take da abin ban ta’ajabi, kuma matasa da manyan mutane a Katsina suna ta furta albarkacin bakunansu kan hakan, inda kusan fa allura za ta tono garma, za a bankado al’amuran tsafe-tsafe da batun bokanci da wasu jami’an gwamnatin suke yi don mallaka da samun amintar shugaban jihar, wato Gwamna Masari.

Leave a Reply