Kimanin Yara Miliyan 13 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Najeriya – UN

2
399

Daga Wakilinmu

Talla

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa Najeriya ta shige gaba, wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin Najeriya, da adadin yara miliyan 13 da ke zaune a gida, ko suke gararamba a gari.

Bayan waɗannan aƙaluma na MDD tuni gwamnatin Najeriyar ta ce ta soma wani bincike domin kididdige yawan yaran da ba su zuwa makaranta.

A cewar Shugaban shirin tallafawa masu karamin karfi na kasar wato National Social Investment Programme da ma’aikatar ayyukan jin kai ke gundanarwa, kawo yanzu an gudanar da aikin kidayar yaran a wasu jihohi.

Dr. Umar Buba Bindir, ya shaida wa wakilinmu cewa, shugaba Muhammadu Buhari da ya ji irin alkaluman da aka fitar na yaran da su zuwa makaranta ya kadu sosai.

”Wannan dalili ne ya sa aka zauna aka yi nazari sosai saboda muhimmancin da ilimi ke dashi a cikin al’umma” in ji Dr bindir.

Ya ce,” Ba tare da bata lokaci ba shugaba Buhari ya bayar da umarni a kan a dauki matakin da ya dace wajen magance wannan matsala, inda ya ce me zai hana a kan makarantu inda su yaran suke yadda ba za su samu wahala wajen samun ilimin ba”.

Ya ƙara da cewa ”Akwai hukumar kididdiga ta kasa tana nan tana bin garuruwa da kauyuka domin tantance yaran da basu zuwa makaranta in ji shugaban National Social Investment Programme.

Dr. Umar Buba Bindir, ya ce wannan matsala ta rashin zuwan yara makaranta ba wai arewacin Najeriya kadai ta shafa ba, ba in da bata shafa saboda binciken da suke yi ya nuna hakan.

Ya ce, “A yanzu mun shirya nan da wata daya zuwa wata biyu cewa in sha Allah za a fara koyawa irin wadannan yara abubuwa hudu, wato turanci da lissafi da yadda za a zauna lafiya da kuma sana’a”.

”Sannan za mu rinka ciyar da su abinci sau uku, kuma an samar da malamai wadanda zasu yi ta koya musu abubuwa tun safe har zuwa dare a kowacce rana”, in ji shi.

Ya ce, iyalan yaran kuma idan an gano su za a sanya su kan tsarin nan na basu naira dubu biyar a kowanne wata.

2 COMMENTS

Leave a Reply