Saratu Ɗan’azumi: yarinya mai ƙwaƙwalwar lissafi ta sami tagomashi

0
522

Tun bayan fitowar bidiyon yarinyar nan ‘yar garin Gaya mai suna Saratu Ɗan’azumi, mutane da dama sun yaɗa bidiyon nata tare sa neman mahukunta su taimaka mata wajen ganin ta sami karatu mai inganci.

Yarinyar dai an nuno ta a wani hoton bidiyo tana yin lissafi a cikin wani yanayi mai ban sha’awa, kuma ba tare da wata wahala ba.

Danna wannan link ɗin don ganin cikakken bidiyon https://youtu.be/QxZSesO8F_Q

Mutane da dama suna tsoron lissafi, to amma sai ga Saratu tana bayar da amsoshin da aka dinga yi mata ba tarr da ta dauki wani dogon zango ba.

A sakamakon haka ne, wata gidauniya mai suna Bashir Ahmad Foundation (BAF) ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatunta, kamar yadda jagoran gidauniyar Malam Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban ƙasa a kan harkar fasahar sadarwa ya bayyana.

Malam Bashir ya bayyana cewa “tun bayan bayyanar bidiyon wannan yarinya mai kaifin basira da hazaka, mai suna Saratu Dan Azumi, wasu da dama suka aika min da videon ta Facebook, Twitter da kuma WhatsApp, bayan na gamsu da hazikancinta daga bisani na umarci Gidauniyar Bashir Ahmad (The Bashir Ahmad Foundation) da tayi amfani da wakilin mu na kauyen da yarinyar ta bayyana, cikin sauki muka samu gidan su sannan wakilan BAF suka ziyarce su a safiyar yau, inda suka samu nasarar ganawa da Saratu, mahaifinta tare da dagacin garin su.

Bayan tattaunawa da fahimtar juna, iyaye da ‘yan uwan Saratu sun amince da yunkurin Gidauniyar Bashir Ahmad (BAF) na daukar nauyin karatunta tun daga Firamari har zuwa Jami’a da yardar Allah.

Zuwa yanzu mun samawa Saratu makarantar da za ta ci gaba da karatu, kuma in Sha Allah daga ranar Litinin za a je makarantar don yi mata rijista da sauran abinda ya kamata.

Haka kuma nan gaba kadan za ta fara daukar horo da koyon fasarar zamani a sabuwar makarantar Gaya Digital Skills Centre.

Allah ya ba mu ikon sauke nauyin da muka dauka, ya kuma kara wadata mu da irin wadannan hazikan yara da anan gaba za su taimaki al’umma baki daya, amin.”

Leave a Reply