Labarin yana gefen ku!

An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

1

An tsinci gawar wani mutum da ba a san kowane ne ba yashe a kan titi a birnin Kano.

An tsinci mutumin a kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin.

A cewar wasu mutane da ke kusa da wajen da aka tsince gawar, suna zargin wasu bata-gari ne suka makure wuyansa da wayar lantarki har sai dai suka tabbatar ya daina numfashi.

Sai dai an garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase domin ba shi agajin gaggawa.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar mai gadi rataye a wata makarantar firamare a Gombe

Ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Leave A Reply

Your email address will not be published.