Labarin yana gefen ku!

Rashin iya lissafi ne ya sa wasu suke cewa an yi cushe a kasafin kuɗin 2024 – Tinubu

1

A makon da ya gabata ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi ƙira da a gudanar da binciken “gaggawa” kan zargin na Ningi.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce rashin ilimin lissafi ne ya sa wasu suke zargin cewa an yi cushe a kasafin kuɗin ƙasar na 2024.

Kasafin na Najeriya na bana ya tashi akan Naira tiriliyan 28.7.

Majalisar Dattawa ta shiga ruɗani a baya-bayan nan, a lokacin da Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya ya yi zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin kuɗin bana.

Kazalika ya yi ƙorafi kan yadda aka raba kuɗaɗen da aka ba mambobin majalisar don yi wa mazaɓunsu aiki.

‘Yan majalisar ta Dattawa sun musanta wannan zargi, suka kuma ɗauki matakin dakatar da Ningi tsawon watanni uku daga majalisar bayan kaɗa ƙuri’a.

KU KUMA KARANTA:Majalisar wakilai ta amince da kasafin kuɗin da zai hana rufe ma’aikatun gwamnati a Amurka

“Waɗanda suke cewa an yi cushe a kasafin, ba su fahimci lissafin ba kuma ba su bi diddigin abin da na gabatar ba – kasafin kuɗi” Tinubu ya ce yayin da yake buɗa bakin azumin watan Ramadana da shugabannin majalisar ta dattawa a fadarsa ta Aso Rock kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito

Rahotanni sun yi nuni da cewa Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya goyi bayan Ningi inda ya ce ana dakatar da shi ne saboda ya faɗi gaskiya.

A makon da ya gabata ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi ƙira da a gudanar da binciken “gaggawa” kan zargin na Ningi.

Kazalika ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin lemar jam’iyar LP, Peter Obi shi ma ya yi ƙira da a gudanar da bincike baya ga kungiyoyi da ke fafutukar tabbatar da adalci irin su CISLAC da su ma suka bi sahu.

Cushe a kasafin kuɗi a Najeriya, batu ne da aka jima ana zargin ana yi inda a lokuta-lokuta ya kan zama abin ka-ce-na-ce a ƙasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.