Idan har Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da ƙudurin kasafin kuɗin, babu makawa sai an rufe wasu ma’aikatun gwamnatin ƙasar.
Majalisar wakilan Amurka ta amince da ƙudurin kasafin kuɗin da gwamnati za ta kashe cikin watanni shida masu zuwa, lamarin da ya sa ake tunanin an ɗauki hanyar kaucewa rufe wasu ma’aikatun gwamnatin.
Yanzu ƙudurin kasafin kuɗin na Dala tiriliyan 1.2 zai nausa zuwa Majalisar Dattawa wacce ake kyautata zaton za ta amince da shi nan da daren Juma’a zuwa ranar Asabar.
Kuɗaɗen da gwamnatin ke kashewa za su ƙare da ƙarfe 12:01 na safiyar Asabar, kodayake, ba lallai ba ne Amurkawa su ji raɗaɗin rufe ma’aikatun gwamnatin idan lamarin ya faɗo a ƙarshen mako.
Idan har majalisar dattawa ba ta amince da ƙudurin ba, babu makawa sai an rufe wasu ma’aikatun gwmnati.
KU KUMA KARANTA:Shugaban Najeriya ya haramta wa jami’an gwamnatin tarayya tafiye-tafiye ƙasahen waje
‘Yan jam’iyyar Democrat da ke majalisar ta wakilai da dama ne suka goyi bayan kasafin a lokacin da aka kaɗa ƙuri’ar da ta nuna mambobi 286 ne suka amince yayin da 134 suka nuna adawa da kasafin.
An jima ana ɗage ƙudurin kasafin kuɗin cikin ‘yan watannin da suka gabata inda akan amince da na wucin gadi domin ma’aikatun gwamnti su ci gaba da aiki.
Ƙiƙi-ƙaƙar da aka fuskanta a majalisun dokokin Amurka kan ƙudurin kasafin kuɗin, ta ƙara fito da rarrabuwar kawunan da ke tsakanin ‘yan Republican masu rinjaye a majalisar wakilai.
Kazalika lamarin ya ƙara fito da irin ƙalubalen da ake fuskanta a duk lokacin da aka ce an raba shugabancin majalisun dokokin ƙasar biyu tsakanin ‘yan Democrat da Republican.