Labarin yana gefen ku!

Najeriya ta lallasa Ghana da ci 2-1 a wasan sada zumunci

1

Ɗan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci ƙwallon farko da bugun fenariti a minti na 38. A minti na 84 ne kuma Ademola Lookman ya zura tasa ƙwallon.

‘Yan wasan Najeriya Super Eagles sun doke takwarorin wasansu na Black Stars a wani wasan sada zumunta a ƙasar Morocco.

Najeriya ta doke ƙasar ta Ghana ne da ci 2-1.

Ɗan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci ƙwallon farko da bugun fenariti a minti na 38.

A minti na 84 ne kuma Ademola Lookman ya zura tasa ƙwallon.

Ghana ta ci ƙwallon ta ne da bugun fenariti ta hannun ɗan wasanta Jordan Ayewa gab da ana kusan tashi a wasan.

Ɗaya daga cikin ‘yan wasan Ghana ya samu jan kati.

Haɗuwar ƙasashen biyu na zuwa ne ƙasa da watanni biyu bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON da aka yi a Ivory Coast wacce ta lashe kofin.

Najeriya ta kai wasan ƙarshe a gasar yayin da aka cire Ghana tun a zagayen rukuni-rukuni, lamarin da ya yi sanadin korar mai horar da ‘yan wasan ƙasar.

Tarihi ya nuna sau 56 Najeriya da Ghana suka kara a fagen kwallon ƙafa a gasa daban-daban da wasannin sada zumunci.

KU KUMA KARANTA:An kuɓutar da almajirai 18 da ‘yan bindiga suka sace a Sakkwato

Ghana ta doke Najeriya sau 25 yayin da ita kuma Najeriya ta doke ta sau 12.

Sauran wasannin an tashi ne babu ci tsakanin ƙasashen biyu waɗanda maƙwabtan juna ne a yankin yammacin Afirka.

Haɗuwa ta ƙarshe da suka ita ce a wasan cin kofin duniya a 2022 da aka yi a Rasha inda Ghana ta fitar da Najeriya daga gasar.

Fitaccen ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen bai samu zuwa wasan ba saboda rauni da ya ji.

Kazalika Taiwo Awoniyi da Tyronne Ebeuhi da Gabriel Osho duk ba su samu halartar wasan na sada zumunci ba.

A ɓangaren Ghana, fitaccen ɗan wasan ƙasar Thomas Partey, shi ma bai samu zuwa wasan ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.