Rufe iyakar Nageriya da Nijar ya sa mun tafka asara – ‘Yan kasuwar Sakkwato

1
198

Tun bayan da aka samu matsalar da ta haifar da rufe iyakokin ƙasa da ƙasa na Nijar da Najeriya ‘yan kasuwa daga cikin Gada dana ƙauyukan Gada suke ta fama da asarori masu ɗimbin yawa.

Zuwa yanzu ‘yan kasuwa, sun yi asara mafi muni a sanadin dakatar lodin manyan motoci Tirela waɗanda suke ɗauke da albasa na tsawon kwanaki ba tare da sun samu ƙetare iyaka ba.

Daga ƙarshe motocin sun dawo gida da kayan bayan kwanaki a tsaye ɗauke da Albasa.

1 COMMENT

Leave a Reply