Ramadan: Fasto Buru Ya Kai Ziyarar Kara Kulla Alaka Tsakaninsu Da Malaman Addinin Musulunci

0
506

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WASU Manyan Malaman Addinin Kirista dake Jihar Kaduna, sun fara ziyarar kara kulla alaka tsakaninsu da wasu Manyan Malaman Addinin Musulunci dake Kasar nan da zummar kara Ƙarfafa zumunci da wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinan.

Babban mai kula da cocin Christ Evangelical and Life Interview Church dake Jihar Kaduna, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana cewa sun fara ziyarar manyan malaman addinin musulunci ne a cikin watan Ramadan da nufin karfafa alakar kiristoci da musulmi a kasar nan.

Ya kara da cewa wannan ya zama musu wani wajibi ne saboda ganin lokacin Azumin watan Ramadan mai albarka ya sake kustowa kuma ya hadu da lokacin Azumin Kiristoci, shi yasa yin hakan zai kara dankon zumunci da fahimtar juna a tsakanin riko da addinan biyu.

A cewarsa, kamar yadda suka yi kira ga mabiyansu da su tashi tsaye wajen gudanar da addu’o’i da kuma yin azumin ranar da Allah zai kawo mana karshen matsalar rashin tsaro da ke kalubalantar rashin zaman lafiya a kasar nan, sun buƙaci su ma al’ummar Musulmi da yin hakan.

Buru ya ce, muna ziyartar manyan malaman addinin Musulunci a gida ne domin inganta kyakkyawar alaka tsakanin Kirista da Musulmi a tsakanin malamai.

Ya ce “Musulmi na yin azumin kwanaki 30 na watan Ramadan, yayin da kiristoci ke gab da kammala rancen kwanaki 40” don haka akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen yi wa kasar addu’a.

“Kamar yadda kuke ganin watan ya riske mu a yanzu tare, kowa yana yin azumi ko Ramadan”.

Malamin addinin Kiristan ya ce, sun hada kai da limamai hamsin domin su hada kai da su a yakin Addu’o’in neman mafita da za a kwashe kwanaki 10 ana yi a fadin Arewa.

A bana, taken ziyarar ita ce: Ziyarar Musanya Dankon Zumuncin Malamai Domin Zaman Lafiya Da Hadin Kai.

Suna addu’a ga sojojin Najeriya da dukkan Jami’an tsaro domin samun nasarar a bisa kokarin da suke a yaki da ta’addanci, ‘yan fashi da makami, kana da masu garkuwa da mutane.

Da yake mayar da martani, babban shaihin malamin Addinin Musulunci nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yabawa fasto yohanna da ya zo gidan ya gaishe su.

Shima wani malamin addinin musulunci Sheick salihu Mai Barota ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyarar tare da godewa maziyartan da suka nuna mana.

Leave a Reply