Matasa Ku Nemi Ilimin Koyon Sana’a – Ustaz Takwashe

2
274

Daga; Musa Muhammad Kutama, Kalaba.

WANI malamin Addinin Islama Sheikh Yusuf Mustapha Takwashe, ya shawarci matasa musulmi da ke neman ilmin zamani da su rika karanta abin da zai zama sana’a gare su

Ustaz Takwashe ya jaddadawa matasa bukatar su nemi ilmin da zai zame musu na Sana’a Mai amfani na zamani a jawabin da ya gabatar makon jiya lokacin da kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Izala ta kasa mai Hedkwata a Jihar Jos reshen Jihar Kuros Riba ya gabatar.

Ya ce “Matasa ku rika karanta abinda idan kun kammala manyan makaranta da jami’oi zai rika zame muku Sana’a ba tare da kun rika dogara da aikin gwamnati ba.” A cewar malamin “ku karanta abinda ya shafi harkar Noma da kiwo da Kuma magunguna ta yadda mutum koda ya Gama karatun ba lallai ne aikin gwamnati ya samu ba mutum yana da Sana’a.”

Ustaz Mustapha Takwashe ya ci gaba da cewa matsalar aikin gwamnati akwai bukatar gwamnati ta daidaita albashin ‘yan majalisa dana malaman Jami’o’i idan aka samu wannan daidaito shi zai magance matsalar wasu na kwasar manyan Kudi matsayin albashi wasu Kuma na korafi a kara musu.

Da ya juya kan matasa, malamin ya hore su da su tashi tsaye su nemi ilmi ta hanyar yin tsayuwar daka su nemi ilmi.

Ya kara da cewa ba matasa ilmi da jawo su a jika zai magance matsalolin shiga karin da bashi da amfani musamman wajen ta’adanci da Kuma sauran aiyukan barna alhali wasu matasan halin yanzu sun wofantar da kansu a cikin al’umma wanda wajibi ne su gyara.

Sannan ya nuna takaicin sa bisa irin yadda matasan yanzu ke watsar da damar da suka samu wajen yin amfani da ita musamman da sune kan gaba wajen yada labaran bogi ko na jita-jita mara amfani ga Al’umma

Daga karshe, ya jawo hankalin matasa su zage damtse wajen neman ilmi da gyara halayen su musamman ta hanyar kaucewa yadda ba zasu fada cikin aikata miyagun dabi’u ba.

2 COMMENTS

Leave a Reply