Daga; Musa Kutama, Kalaba.
AN yi Kira ga matasa da al’ummar musulmi da suyi amfani da falalar goman karshe da Kuma darussan da suka koya a wannan wata na Ramadan da muke yin bankwana dashi, su nemi Dukiya ta hanyar Halal sannan a guji nemanta ta hanyar Haram.
Ustaz Muhammad salihu Musa Mangu ne ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar na mahadarar kwamitin wa’azin matasa na jungiyar Izala ta kasa mai hedkwata a Jos reshen Jihar Kuros Riba wanda aka shirya ranar Lahadi 24 ga watan Afrilu wannan shekara karo na takwas.
Malam salihu musa Mangu ya ci gaba da cewa a nemi dukiya ta hanyar Halal, kana ya buƙaci matasa da su nemi sana’a da aikin yi domin tana zama kariya ta mutunci da Kuma kaucewa fadawa cikin aikata haram.
Hakazalika, ya kara da cewa ciyar da kai da Kuma iyali ta hanyar Halal da Kuma dukiyar da aka ciyar da ita ta hanyar Halal Allah na sanya mata albarka.
Da ya juya kan illar tara Dukiya ta Hanyar Haram, malamin ya jawo hankalin al’ummar musulmi da Kada wadanda suka tara dukiya ta hanyar wuru-wuru ko ta satar dukiyar gwamnati dama cin hanci da rashawa domin duk dukiyar da aka tara ta kan wannan fanni ba abinda zai haifarwa irin wadannan mutane face tarin zunubi da Kuma haduwa da fushin Ubangiji.
Ustaz Muhammad salihu Musa Mangu ya kara da cewa mutane da suke tara dukiya ta hanyar haram suji tsoron Allah domin duk dukiyar da aka tara ta hanyar Haram Allah madaukakin sarki zai tambayi wanda ya tara wannan dukiya yadda ya tara ta don haka kaicon masu tara dukiya ta hanyar wuru-wuru ko karma-karma koma satar dukiyar gwamnati.
A karshe, malamin ya jawo hankalin al’ummar musulmi da lallai su nemi sana’a da Kuma dukiya ta hanyar halal kuma su ciyar da ita ta hanyar halal kana a kaurace wa Haram.