Nura Golden Ya Yi Fice Wajen Taimakawa Al’ummar Lere – Mahe Kwaftara

0
299

Daga; Isah Ahmed, Jos.

WANI shugaban matasa, kuma Shugaban Kungiyar direbobin motocin J5, na Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Malam Mahe Alhassan Kwaftara, ya yaba wa fitatcen Dan kasuwar nan, Alhaji Nura Danladi Golden da ke zaune a garin Saminaka, kan irin taimakon da yake yiwa al’ummar Karamar Hukumar Lere, a fannoni daban daban.

Malam Mahe Kwaftara, ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu inda ya bayyana cewa suna matukar jin dadi da farin ciki, kan irin taimakon da Alhaji Nura Danladi Golden yake yiwa al’ummar Karamar Hukumar ta Lere.

Ya ce “babban aikin da wannan bawan Allah ya yi a ‘yan kwanakin nan, shi ne cike ramukan babbar hanyar gwamnatin tarayya da ta ratso wannan yanki, daga Unguwar Bawa zuwa garin Saminaka.”

“Kafin ya gyara wannan hanya, mutane masu abubuwan hawa suna matukar shan wahala. Amma yanzu sakamakon gyara wannan hanya da ya yi, mutane masu abubuwan hawa suna bin wannan, hanya hankalinsu kwance.

Har’ila yau ya ce Alhaji Nura Golden ya yi fice wajen taimakawa da miliyoyin naira, wajen gina masallatai da makarantun islamiyya da taimakawa marayu da mukata a wannan yanki.

“A yanzu a watan Azumin nan da ya shigo, yana nan yana ta tallafawa mabukata da marayu da kayayyakin abinci kuma abin mamaki, duk wadannan abubuwa da yake yi, baya son Jama’a su sani, domin yana yi don Allah. Mu dole mu fadi wadannan ayyukan alheri da yake yi, kuma mu yi kira ga Jama’ar wannan yanki, su yi masa addu’a. Kuma mu yi kira ga yan siyasa da sauran masu hannu da shuni, su yi koyi da wannan bawan Allah”.

Leave a Reply