Fasto Buru Ya Zama Gwarzon Gasar Cin Kyautar Makon Mu’amalar Addinai Ta Duniya

0
349

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WANI futatcen malamin addinin kirista dake Kaduna Arewacin Najeriya, Fasto Yohanna Buru, ya zama zakaran gwajin dafi na Duniya, yayin da ya lashe gasar cin kyautar Makon Mu’amalar Addinai ta duniya na shekarar 2022, wanda Sarki Abdullah na biyu da Yarima Ghazi bin Muhammad na kasar Jordan suka shirya.

An wallafa sakamakon kyautar gasar ne a shafin yanar gizon kungiyar inda ta bayyana cewa wannan ita ce kyauta mafi girma a tarihin rayuwarsa kuma ta zo a daidai lokacin da zai kara kaimi wajen daukar karin yakin neman zaman lafiya a wurare daban-daban.

Babban malamin mai kula da cocin bishara ta Kirista da shiga tsakani na rayuwa dake Sabon Tasha, Arewa maso yammacin Najeriya, kuma shugaban kungiyar zaman lafiya ta kasa, fasto yohanna buru ya yi nasarar zama wanda ya lashe lambar yabon ne ta bana ne ta Makon zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ta kasa da kasa ta 2022.

Da yake jawabi, Fasto Buru, ya ayyana nasarar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a matsayin wanda ya lashe gasar makon na Mu’amalar ta duniya na 2022, kana ya yi godiya ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), Muryar Najeriya (VON), da Kamfanin Jaridar New Najeriya Newspapers (NNN) bisa gagarumin gudunmuwar da suka bada na wallafa labaran a cikin wannan makon ba.

Ya ce “Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) da Muryar Najeriya (VON), sabuwar Jaridar New Najeriya Newspapers, Jaridar Tribune ta taimaka mana wajen yada wannan taron na tsawon kwanaki 7 da nufin wayar da kan miliyoyin ‘yan Najeriya gida da waje.”

“Ba zan iya mantawa da kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya da kungiyar ‘yan jarida ta zaman lafiya a fadin duniya da jakadan zaman lafiya na sa-kai da Jami’an zaman lafiya a duk fadin duniya saboda sadaukarwar da suke yi na yau da kullum na karfafa hadin kan addinai a tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban ba.”

Ya kara da cewa, a cikin kwanaki 7 na Makon, ya samu damar shirya abubuwa da dama da suka hada da daukar gangamin makon mabiya addinai a makarantu da dama, da al’ummomi, kasuwanni, cibiyar kallon kwallon kafa, bangaren mota, tashar jirgin kasa, da dai sauransu kamar wasannin kwallon kafa da dai sauransu. Hakay, juriya a tsakanin ƙungiyoyin masu gaskiya daban-daban waɗanda ke Kokarin haɓaka juriya na addini, samar da kyakkyawar fahimta, kana da zaman lafiya da gafara.

Ya kara da cewa, tawagarsa sun ziyarci asibitoci da dama kuma sun ba da gudummawar magunguna kyauta da wasu kudade na tallafi ga majinyata.

Ya ce, kyautar za ta kara masa kwarin gwiwa wajen samar da karsashi wajen kara kulla zaman lafiya a makarantu da kuma cikin wasu al’ummomi, da nufin koya wa matasa hanyoyin dasa iri na zaman lafiya, Jituwa da jin dadi.

“Na yi matukar farin ciki ga wadanda suka shirya taron, kuma a matsayina na jakadun zaman lafiya, zan isar da sako a fadin kasar.”

A cewarsa, Alkalan sun karbi rahotanni 85 da aka mika don kyautar daga daruruwan abubuwan da aka gudanar a fadin duniya. Wannan wani gagarumin yunƙuri ne idan aka yi la’akari da ci gaba da tasirin cutar ta Covid-19 a duniya.

Buru ya bayyana jin dadinsa da godiya ga masu shirya taron shekara-shekara na mako da nufin hadin kai na duniya tare da yin kira ga kungiyoyi masu zaman kansu, Kungiyoyin farar hula su goyi bayan gwamnati a kodayaushe wajen samar da zaman lafiya da hadin kai a fadin Jihohi 36 na Najeriya.

A karshe, Fasto Yohanna Buru, ya kara da yin godiya ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Jaridar New Nigerian Newspaper (NNN), Voive of Nigeria (VON) da Rediyon Najeriya kaduna FRCN bisa tallafin da suka bayar na yada makon haduwar Mu’amalar addinai da kuma sakwannin jituwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya, tare da godewa dukkanin kafafen yada labarai na Najeriya da na duniya wadanda sun hada da BBC, DW-Germany Radio International, Muryar Amurka da kuma Sashen Hausa na Faransa RFI domin bayar da gudunmuwar da za a rika yadawa a duk mako.

Leave a Reply