ABG Ya Taimakawa Wata Gidauniyar Mata Da Naira Miliyan 1.5

0
451

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON dan majalisar tarayya Honarabul Shehu Bawa, wanda aka fi sani da ABG, ya baiwa wata gidauniyar ci gaban mata a mazabar Kaduna ta Arewa kudi naira miliyan daya da rabi a wani mataki na rage radadin talauci a tsakanin al’umma.

A yayin da yake yabawa wannan shiri na gidauniyar ta musamman kan tasirin sana’o’in hannu ga mata, ABG ya jaddada kudirinsa na ci gaba da bayar da gudummawar kasonsa domin inganta rayuwar matasa da mata a mazabar Kaduna ta Arewa da bayanta har sai an magance zaman banza.

An kafa kungiyar da aka fi sani da Badarawa Development Foundation, a cewar ma’ajin ta, Umar Adamu domin zama cibiyar koyar da sana’o’i ga mata wadanda ya ce su ne suka fi fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki a fadin kasar nan.

Adamu ya bayyana cewa gidauniyar a sabon aikinta na baya-bayan nan ta sami damar horar da mutane sittin a kan harkar girke-girke, mutane hamsin aka koya musu saka da kuma wasu arba’in kan harkar sana’o’in kwalliya, wanda ya sa adadin mata 150 da suka ci gajiyar shirin.

Ma’ajin, yayin da yake mika godiyarsu ga ABG bisa bada gudumawa don samar da abin dogaro ga matan, ya bukaci sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da dan siyasar wanda ya bayyana a matsayin mai baiwa da karamci, ta hanyar zaman wani ginshikin tallafawa al’umma domin ya sanya damuwar talakawa a zuciyarsa .

Tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa daga shekarar 2011 zuwa 2015 ya bada tabbacin shirinsa na cigaba da baiwa jama’a karfin gwiwa har sai an dakile matsalar zaman banza da ya lura ta zama barazana ga al’ummar Najeriya.

“Na yarda cewa rashin aikin yi ya haifar da munanan abubuwa a cikin al’ummominmu da suka hada da rashin tsaro, shaye-shayen kwayoyi, karuwanci da sauran munanan dabi’u .

“Idan ya zama dole mu kawar da wadannan cututtuka na al’umma, dole ne mu dauki batun rashin aikin yi da muhimmanci a tsakanin al’ummominmu don haka yawancin matasan mu da mata dole su shiga cikin wani nau’i na sana’a ko wata.

“Wannan wata ‘yar karamar hanya ce da na dauka domin fitar da mutane daga kan tituna da samar musu da hanyoyin samun abinci domin su kasance masu amfani ga iyalansu da sauran al’umma baki daya.

“Na kuma kuduri aniyar ci gaba da yin hakan don samun nasara har sai kokarinmu ta samu nasara,” in ji shi.

Leave a Reply