Najeriya ta tsallaka zuwa wasa na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Afirka

0
132

Daga Ibraheem El-Tafseer

Najeriya ta samu damar tsallakawa zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin ƙasashen Afirka, bayan samun nasara a kan ƙasar Angola da ci 1 – 0 a wasan da suka buga da yammacin ranar Juma’a.

Ɗan wasan Najeriya na gaba, Ademola Lookman ne ya samu damar zura ƙwallon ɗaya tilo a ragar Angola, a minti na 41 da fara wasan.

Yanzu da wannan nasarar Super Eagles ita ce ƙasa ta farko da ta samu tikitin kaiwa wasan na kusa da na ƙarshe.

Najeriyar za ta fafata da Afirka ta Kudu ko Caper Verde waɗanda za su buga wasan dab da na kusa da na ƙarshe ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: CAF za ta yi bincike kan rikicin da ya faru bayan wasan Maroko da DRC a gasar AFCON

Wannan ne karo na 20 da Najeriya ke halartar gasar a tsawon shekaru 34 da aka yi ana gasar ta cin kofin ƙasashen nahiyar Afirka.

Najeriya, wadda ta lashe kofin gasar sau uku kuma yanzu haka mai matsayi na 42 a duniya, ta kasance wadda ake ganin za ta iya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023, tun bayan da ƙasashen da ke yi wa Najeriyar barazana suka yi waje-rod.

Tuni dai Morocco mai matsayi na 13 da Senegal mai riƙe da kofin gasar wadda ke matsayi na 20 da Tunisia ta 28 da Aljeriya ta 30 da Masar ta 33, duk sun riga sun yi waje daga gasar.

Da ma dai tun gabanin wasan Najeriya da Angola na yammacin Juma’a, wata ƙididdigar da kamfanin Opta ya yi, ta nuna Najeriya ce ke kan gaba wajen damar lashe gasar – da kusan kashi 28.8% – kuma tana da damar doke Angola da kashi 55.5 cikin ɗari a cikin mintuna 90.

Leave a Reply