Muna Son Samun Sababbin Hanyoyin Noman Masara A Najeriya – Bello Annur

0
444

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SHUGABAN masu kokarin habbaka Noman Masara a tarayyar Najeriya Alhaji Bello Abubakar Annur Funtuwa, ya bayyana kokarin da suke yi domin kara habbaka Noman Masara a fadin kasar baki daya da cewa domin dogaro da kai ne.

Alhaji Bello Abubakar Annur, ya shaidawa manema labarai hakan ne a lokacin da yake ganawa da su a wajen babban taron bitar da suka shiryawa mambobin kungiyar a Kaduna.

Alhaji Bello Annur ya ci gaba da cewa an shirya wannan taron fadakarwa da ake yi a yanzu haka a garin Kaduna ne domin fadakar da mambobinsu da kuma sauran manoma na kasa baki daya irin romon da ke tattare da yin amfani da fasahohin zamani wajen yin Noma.

“Kasancewar ba a dade da yin zaben sababbin shugabanni a kungiyar ba don haka aka ga ya dace a yi wa sababbin shugabannin taron bita domin kowa ya fadaka a game da Noman zamani da kuma hanyoyin da ya dace manoma su tunkara musamman masu Noman Masara”.

Ya kara da cewa taron kuma zai taimaka masu wajen sanin yadda za su tafiyar da shugabancin kungiyar kasancewa an yi sabon zaben shugabanni ne.

A game da batun matsalar tsaro kuwa, Bello Annur ya shaidawa manema labarai cewa, ” hakika kamar yadda kowa ya Sani akwai matsalar tsaro a kasa musamman a yankin arewacin Najeriya, amma duk da hakan an godewa Allah domin an yi Noma kuma an samu amfani kwarai duk da dai matsalar ta kasance wasu daga cikin manoman da suka fara aikin Gonar suna ji suna gani abin ya gagare su saboda irin yadda matsalar take tafiya, wasu sun bar Gonakan sun ta fi wasu kuma bayan sun yi Noman sun girbe amfanin Gonar amma su je su gyara shi sai lamarin ya zama wata matsala daban domin abin ya gagara, har wasu an Kona masu Gonakan kuma da yawa daga cikin manoman Masara abin ya shafe su saboda hakan zamu ce an samu matsaloli amma duk da hakan za mu ce sai godiyar Allah domin an yi Noman kuma an same shi”.

A game da batun Dalar Masarar da aka tara a Kaduna kuwa domin a kara wa manoma kwarin Gwiwar ci gaba da zage damtse domin Noma Masara kuwa, Bello Annur ya kara da bayanin cewa hakika an samu ci gaba kwarai a wajen batun Noman Masara domin na farko ma an samu yin Dalar Masarar fiye da irin wadda aka samu a bara, domin a ba na an samu yin Dala guda Ashirin da biyu da ake saran zuwan shugaban kasa domin ya kaddamar a Kaduna wanda hakan ba karamin ci gaba aka samu ba.

“Kuma duk Masarar da aka tara an karbo ta ne daga hannun Manoman da aka ba kayan Noma suka Noma kuma za a sayar wa masu kamfanonin sarrafa ta suma su ci gajiyar shirin da Gwamnati take aiwatarwa, duk kamfanin da aka Sayarwa zai Sanya wa Gwamnati kudin ta ne a cikin Banki kawai ya dauki Masara  ya ta fi da ita kamfaninsa domin ya sarrafa kasa da jama’arta baki daya su samu amfani kamar yadda duk dan kasa nagari ke bukata”. 

Leave a Reply