Connect with us

Noma

An Kaddamar Da Takin Zamani Na Dangote

Published

on

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana kamfanin Dangote a matsayin katafaren kamfanin da ke kokarin bunkasa harkokin Noma a Najeriya, Afrika da duniya baki daya.

Injiniya Dokta Mansir Ahmad ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da Takin Zamani na Uriya wanda kamfanin Dangote ya samar domin ci gaban manoma da kasa baki daya.

Injiniya Mansir Ahmad, ya kaddamar da Takin Zamanin a madadin kamfanin Dangote, domin manoma su samu damar ci gaba da amfani da shi a wajen Noman rani da na Damina.

Ya ce “Hakika babban abin da wannan kamfanin ya Sanya a gaba shi ne bunkasa harkokin Noma da sauran dukkan bangarorin kasuwanci a kasa baki daya.”

An kuma tabbatar da cewa ana kai Takin Zamani na Dangote zuwa wadansu kasashe na duniya, kuma hakan ya faru ne sakamakon irin ingancin da Takin yake da shi.

An ci gaba da cewa an samar da Takin zamanin Dangote ne bayan gudanar da kyakkyawan bincike domin samun inganci da yanayin kasar Noma ta hanyar yin amfani da Kimiyyar zamani don haka duk wanda ya yi amfani da Takin zai samu biyan bukata.

Injiniya Mansir Ahmad ya kuma yabawa masu shirya kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna bisa damar da suka ba kamfanin Dangote ya kaddamar da Takin zamaninsu a hukumance domin hakan shi ne na farko, “saboda an fara yin sa ne watanni shida ko Bakwai da suka gabata”, inji Mansir Ahmad.

Mansir Ahmad ya kuma tabbatarwa manema labarai cewa katafariyar matatar mai ta Dangote za ta rika samar da miliyoyin litar mai da zai wadanci kasar nan, kuma mai mai matukar inganci saboda ko a kasashen turawa na tarayyar Turai aka kai man za a iya sayar da shi domin ingancinsa daya ne da na man kasashen tarayyar Turai.

Injiniya Mansir Ahmad ya kuma bayyana cewa nan gaba kadan kamfanin Dangote zai kara samar da wadansu abubuwan da jama’a za su ci gaba da yin amfani da su, kamar Man fetur da dangoginsa da kuma mota kirar kamfani da sauran abubuwa da dama kasancewar kamfanin na kokarin samar da sababbin abubuwan amfanin jama’a a koda yaushe.

Kamfanin Dangote na yin Suga,Magi,Gishiri,Sumunti da sauran kayan dandanon abinci kala kala, kuma nan gaba za su ci gaba da samar da wadansu kayayyakin da dama.

A waje daya kuma manoma sun yaba wa kamfanin Dangote bisa irin kokarin kara habbaka harkokin Noman da yake yi, wanda hakan ke ba su damar ci gaba da fadada harkokin Nomansu.

“Hatta da farashin Takin zamani a shekarar da ta gabata Takin Yuriya na kamfanin Dangote ne ya cece manoman Najeriya kowa ya samu yin Noma a cikin sauki da kwanciyar hankali”, inji Manoma.

1 Comment

1 Comment

  1. Abdullahi Ibrahim Balanti Makarfi

    March 7, 2022 at 6:52 am

    Allah yasa mu amfana da wannan tagomashi na takin dan gote, amm abun duba anan shine a taimaki talaka ya samu takin cikin sauki da yalwa, dan inganta harkar noma a kasar mu Najeriya tare da duniya baki daya, Allah yasa mu dace da rabo mai amfani duniya da lahira Amin summa amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Bagudu ya halacci taron bunƙasa harkar noma a Abuja

Published

on

Daga Idris Umar, Zariya

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi na ƙasa a ranar Talata 16/04/2024, Ya halarci wani shiri na musamman a babban birnin tarayya Abuja domin bunƙasa sha’anin harkokin ayukkan gona a faɗin Najeriya.

Shirin wanda yake ƙarƙashin gwamnatin ƙasar Jamus (Germany ) da kuma ƙungiyar GIZ zai bayar da gagarumar gudumuwa wajen bunƙasa sha’anin ayukkan gona a Najeriya.

Bagudu ya bayyana alfanun da ke akwai ta haɗaka da ƙungiyoyi ire-irensu GIZ ta hanyar musayar ilmi da amfani da zamani wajen cimma manufa, Bagudu ya ƙarfafawa mutanen da suka halarci shirin da su rinƙa shirya taron ƙara wa juna sani domin cimma kyakkyawar manufar ciyar da ƙasa gaba.

KU KUMA KARANTA: Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano

Bagudu ya ƙara fayyace cewar haɗaka na da matuƙar muhimmanci domin ta hakan ne za’a samu ci gaba a fannin tattalin arziƙi da ci gaba a Najeriya.

Continue Reading

Labarai

Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano

Published

on

Wasu manoman tumatur a ƙaramar hukumar Bagwai ta jihar Kano, sun koka kan yadda tsutsa ke lalata musu amfanin gona.

Manoman sun ce sun yi asarar amfanin gona da ta kai kusan Naira miliyan 500. Sun kuma ce tsutsar ta shafi kusan hekta 1000 na gonakinsu.

Wani manomin tumatir, Bello Idris ya ce suna cikin wahalhalu kan yadda tsutsar ta addabe su.

”Za mu nome tumatir mu sayi taki 50,000, mu kuma sayi maganin feshi 10,000 da man fetur amma duk a banza,” in ji shi.

Ya yi ƙira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki da kuma gano inda matsalar take.

KU KUMA KARANTA: Jihar Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma

Haka-zalika, shi ma Sama’ila Bello mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce tsutsar na lalata musu amfanin gona cikin lokaci kankani.

“Muna so gwamnati ta taimaka mana a duba a ɓangaren iri ne ko maganin feshi ne ba a sayar da mai kyau,” in ji Bello.

Continue Reading

Labarai

Jihar Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma

Published

on

Gwamnatin Kebbi ta ɓullo da shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin sauƙaƙa musu yin wahalar noma a jihar.

Kwamishinan Noma na jihar, Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin ta samar da haujin noma, inda aka farfaɗo da aikin noma domin jihar ta cigaba da riƙe kambunta a ɓangaren noman shinkafa a Najeriya.

Saboda haka ne ta gina ƙaramin wurin noma na zamani a ƙananan hukumomin Argungu da Fakai a garin Mahuta.

Wannnan a cewarsa, ƙari ne a kan tallafin noman rani da manoman shinkafa 30,000 da masu noma masara 7,500 da kuma masu noman rogo 2,000 suka samu daga gwamnatin.

KU KUMA KARANTA: An ceto manoma 16 daga hannun masu garkuwa da mutane a Neja

Ya ƙara da cewa gwamnatin jiha ta biya kasonta na naira miliyan 350 a cikin shirin RAAMP, wanda zai samar da hanyoyin mota masu tsawon kilo mita 240 domin manoma su samu saukin sufuri, gwamnati ta sanya miliyan 350 a shirin.

Shehu Mu’azu ya sanar da hakan a taron manema labarai na sati-sati da ma’aikatar yada labarai ta shirya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like