‘Yan Majalisar Dokoki Ba Su Yi Amfani Da Dattako Wajen Fuskantar Koke Koken Mata Ba – Aisha Buhari

0
363

Daga Wakilinmu.

UWARGIDAN shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta tofa albarkacin bakinta akan ce-ce-ku-ce da ke gudana a kasar sakamakon yin watsi da dokokin da ka iya ba mata damar samun kashi 35 cikin 100 na kujerun siyasa.ABUJA, NIGERIA — 

A wata takardar bayani da ta aiko da ita wa manema labarai ta yanar gizo, a ciki har da Muryar Amurka, Aisha Buhari ta bayyana bakin cikinta tare da nuna alhini akan abin da ta kira rashin adalci daga bangaren ‘yan Majalisar Dokokin kasar, to saidai kwararru a faninn siyasa na cewa abin da mata ke nema ba haka dimokradiya ta gada ba.

Shawarar da Majalisar Dokokin Najeriya ta zartas akan shaánin takarar mata a kundin tsarin mulkin da majalisar ta yi wa gyarar fuska, ta ci gaba da fuskantar Allah wadai daga masu ruwa da tsaki a Najeriya, a ciki har da Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya Aisha Buhari.

Aisha Buhari
Aisha Buhari

A wata takardar bayani, Aisha ta ce ‘yan Majalisar Dokoki ba su yi amfani da dattako wajen fuskantar koke koken mata ba. Aisha ta ce matakin bai yi wa mata dadi ba, hasali ma, ganin yadda ita da matar Mataimakin Shugaban kasa, Dolapo Osinbajo suka nuna goyon bayansu ga dokar, ya kamata yan majalisa su dube su da idon rahama, su amince da wasu bangarorin dokar. Aisha ta ce za su sake zage damtse wajen tuntuba da yi wa dokar gyara yadda za ta samu karbuwa a zaurukan Majalisar nan gaba.

Ita ma tsohuwar Ministar Ma’aikatar Mata, Aisha Ismail ta bayyana raáyinta a game da wannan batun, inda ta ce za a hadu a dandalin zabe.

To saidai masanin harkokin siyasar kasa da kasa kuma malami a Jami’ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi nuni da cewa ba a taba yin dimokradiya da son zuciya ba.

Mata sun fito sun yi dafifi a kofar Majalisar inda suka nemi a sake duba dokokin a gyara su, domin matan Najeriya na fitowa kwansu da kwarkwatansu lokutan zabe suna kada kuri’a amma ba su cika samun manyan mukamai ba.

Leave a Reply