Gwamnan Jihar Kwara Zai Jagoranci Kwamitin Mutane 8 Domin Duba Batun Zaben Shiyya A APC

1
413

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SHUGABAN kwamitin rikon Jam’iyyar APC na kasa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron APC na kasa wanda ya kasance kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da nadin kwamitin da zai yi aiki a kan batun shiyya – shiyya gabanin babban zaben Jam’iyyar.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Sanata Dokta, John Jemes Akpanudosehe sakataren babban kwamitin shirye shiryen babban zaben na kasa.

Ga dai sunayen mutanen kamar haka:

1.Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahaman AbdulRazak a matsayin shugaba.

  1. Mataimakin shugaban majalisar Dattawa ta kasa Ovie Omo Agege a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.

3.Farfesa Etim Nyang a matsayin Mamba.

  1. Dokta MB Shehu a matsayin mamba.
  2. Kwamared Mustapha Salihu a matsayin mamba.
  3. Sanata Teslim Folarin a matsayin Mamba.
  4. Alhaji Sadeeq Sule-Iko Sami a matsayin Mamba.
  5. Mataimakin Gwamnan Jihar Anambara Nkem Okeke a matsayin Sakatare.

Ana kuma saran kwamitin ya mika rahotansa a ranar Litinin 7 ga watan Maris, 2022.

1 COMMENT

Leave a Reply