Manoman Jihar Jigawa Suna Amfana Da Kungiyar AFAN- Hussaini Mahmoud

0
356

JABIRU A HASSAN, Daga Dutse.

JAMI’IN Hulda da jama’a na biyu a Kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Jigawa Malam Hussain Mahmoud Dutse ya sanar da cewa manoman Jihar zasu ci gaba da amfana da shirye-shiryen kungiyar na bunkasa noma a fadin Jihar.

Ya yi wannan tsokaci ne a wata ganawa da wakilinmu, inda ya jaddada cewa kungiyar AFAN reshen Jihar Jigawa tana da shugabanni nagari kuma masu kishin ci gaban manoma Kamar yadda suke gudanar da aiyukan su na yau da kullum.

Ya ce “manoman Jihar Jigawa sune a zuciyar kungiyar ta AFAN, sannan tana kokari ne wajen samar da dukkanin abubuwan da manoma zasu amfana dashi wajen bunkasa noman su, don haka ake ganin ci gaba ingantacce a kowane lungu da sako na fadin jihar ta Jigawa wanda hakan abin alfahari ne.”

Malam Hussain Mahmoud ya kuma bada misalai na yadda kungiyar AFAN da gwamnatin Jihar Jigawa ake tafiya tare wanda kuma hakan ya kawo ci gaba a harkar noma da bunkasar tattalin arziki da kuma samar da aiyukan yi rani da damina kamar yadda ake gani a yau.

Ya yi amfani da wannan dama inda ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar da ma’aikatar gona ta jihar da ofishin ma’aikatar gona ta tarayya dake jihar Jigawa da kuma shugaban kungiyar AFAN Alhaji Idris Yau Mai Unguwa saboda kokarin da ake yi wajen kyautata fannin noma a Jihar.

Leave a Reply