Makarfi Mutum Ne Mai Magana Daya – Wike

0
306

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

GWAMNAN Jihar Ribas Nyeson Wike, ya bayyana Sanata Ahmad Muhammad Makarfi a matsayin mutum mai magana daya a koda yaushe.

Nyeson Wike ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo ziyarar girmamawa da kuma fatan alkairi ga Sanata Makarfi tun bayan da ya dawo daga kasar Ingila neman magani.

“Mun yi magana da shi ya ce Mani ya na Ingila neman magani, amma ya ce ga shi a Abuja duk da haka na gaya masa zan zo gida Kaduna in gan shi tun da ya dawo lafiya, muna godiya ga Allah da hakan”.

“Babban abin dubawa a halin yanzu shi ne yayan jam’iyya su samu hada kansu wuri daya ba maganar tsayawa takara ba ne lokaci zai zo nan gaba kadan, saboda koda an taayar da wani dan takara daga yankin Kudu ko Kudu maso Yamma idan ba a hada kan yan jam’iyya ba ta yaya za a samu nasara”, inji Wike.

Ya ci gaba da cewa jam’iyyar PDP ce yan Najeriya ke bukata domin ita ce ta dace da su, don haka a hadu wuri daya kawai ayi aiki tare domin na san Sanata Makarfi mutum ne mai kokari kwarai”.

“Kamqr dai yadda kowa ya Sani ba zamu bari kowa ya kashe kasar nan ba don haka aikin hadin kai ne kawai ya dace da mu baki daya”, inji Wike.

Da yake nasa jawabin Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, cewa ya yi kamar yadda ya san Gwamna Nyeaon Wile da kokari hakika babu wanda zai dauke kokarin daga gare shi.

Makarfi ya ci gaba da cewa ya san lokacin da yake shugaban kwamitin rikon PDP Gwamna Wike ya yi duk abin da zai iya domin ya taimaka mana ni da kwamiti na, son haka zamu iya ci gaba da aiwatar da abin da muka yi kamar can baya da nufin samu mu lashe zabe.

Leave a Reply