Barazanar Hana Kai Shanu Kudu: ‘Yan Kasuwar Kudanci Na Maraba Da Hakan

0
496

Daga; Musa Muhd Kutama, Kalaba.

KUNGIYAR dake fafutukar kafa kasar Biyafara ta sha yiwa gwamnati da wasu al’ummar Kasar nan aika-aika na ta’addanci da sunan kafa kasar Biyafara wanda ko a makon da ya gabata, anyi zargin Yan kungiyar ne suka kai harin ta’adanci a wani ofishin ‘yan sanda jihar Imo wanda shi ne harin ta’addanci na farko a wannan watan sabuwar shekara nan.

Baya ga kisan dauki dai-dai dana mummuke da suke yiwa direbobin motoci da Kuma kananan Yan kasuwa dake cin rani a Jihohin da aiki ta’addanci yafi kamari a kudu maso Gabas wato Anambra da Imo. Matsalar ta’addanci a Jihar Imo, ana zargin wani babban dan siyasar Jihar mai rike da madafun iko a yanzu shi da kanen sa ne suke ruruta wutar lamarin da Hope Uzodinma gwamnan Jihar Imo ya fito karara ya ce sam ba zata sabu ba.

Matsalar lalacewar tsaro a wannan yankin yadda yake shafar Yan Arewa mazauna yankin ya kai hatta manya da sarakunan Hausawan da mataimakin gwamna na musamman kan harkokin Yan Arewa ana zargin sun kasa tabuka komai wajen magancewa Yan Arewa matsalolin su.

Ko a watannun baya ma sai da kungiyar IPOB ta yanke hukuncin daga 22 ga watan Janairu 2022 babu wasu Dabbobi ko kayan abinci da zasu sake shigowa yankin kudu maso gabas .

A kan haka ake tambaya shin Mai ya sanya yan Arewa mazauna can ba zasu kaurato su dawo gida ko wasu Yankunan na kudu maso kudu ko Yamma ba, kana mai zai hana yan kasuwar su zabi Jihohin Binuwai da Nasarawa ko Neja ko kuma Kogi masu makwabtaka da kudu maso Gabas su kafa kasuwar su wanda a kan haka wakilin mu na kudanci jiwo ta bakin wasu yan kasuwar mazauna yankin kudu maso Gabas da kudu maso kudu.

An samu mabanbantan ra’ayi kashi 70 cikin 100 basu goyon baya yayin da kashi 30 kuma ke son haka.

Alhaji Ahmad Rufa’i na daya daga cikin manyan Yan Arewa mazauna kudu maso Gabas ga yadda ya fahimci lamarin da ra’ayin sa kan haka cewa sun godewa Allah da zaman su anan, amma har yanzu dai akwai fan abinda ba a rasawa domin ko a shekaran jiya yan aware sun kaiwa yaran su hari har sun jikkata mutum biyu, sun watsa kasuwar.

“Sun kore su sunce musu ba mun gaya maku bamu son kara ganin Wani dan Arewa a nan ba? Yaran sunzo da adduna suna neman Inda Hausawa suke.”

Batun kafa wata kasuwar Dabbobi a Wani yankin Arewa ta tsakiya Alhaji Amadu Rufa’i yace wannan Batu na manyan kasa shi baya goyon baya domin ai arzikin ma’adini ne yasa suke masu gori tun da Arewa ma tana da shi, ai kamata yayi ace an tono shi a huce takaici.

Idan za’a tuna lokacin mulkin Marigayi Sa Ahmadu Bello sardaunan sakkwato, anyi yunkurin kafa kasuwar shanu a Garin Makurdi hedkwatar Jihar Binuwai a yanzu amma abin ya ci tura.

A nasa bangaren, Atiku Abubakar Jos Wani dan kasuwa mazaunin kudu maso Gabas ya ce, matukar ana gurgunta kasuwanci tsakanin kudu da Arewa, ko wane bangare zai ji jiki.

“kamar su yadda suke kwadayin nama idan ba’a kawo ba, ai na mutum zasu koma ci. Gaskiya barazanar babu wani tasiri da zata iyayi kamar irin yadda naga matakan tsaro da aka dauka nasan kashi 70 cikin 100 ba zasu goyi da bayan a kafa kasuwar a makwabta jahohin kudu maso Gabas ba na Arewa, amma nasan 30 cikin dari zasu so hakan”

A jihar kuros riba kuwa, Alhaji Ibrahim Mai yin safarar tumatir daga Arewa zuwa kudu maso kudu ya nuna matukar farin ciknsa idan ma aka kauracewa yankin kudu maso Gabas da kai musu ko wane irin kayan abinci.

“Mun huta wulanci da cin zarafin da su ke yi mana idan mun dauko kayan sayarwar mu, ni nama fi son a kaurace musu mu kafa ta mu kasuwar kan iyaka tsakanin Jihohin Binuwai ko Kogi ko Nasarawa masu makwabtaka in yaso suzo su saya.” Inji shi

Abin jira a gani shi ne idan watan Afrilu ya kama ko kurarin na zai yi tasiri lura da cewa a shekarun baya tunkurin jiyin milkin Gideon Okar da bayyi nasara ba a wasu sassan kudu maso kudu, an ba yan Arewa wa’adin su koma Inda suka fito da Kuma na soke zaben 12 ga watan Yuni 1993.

Leave a Reply