Fulani Makiyaya Na Kokawa Da Tarar Naira Dubu 100 Ga Kowane Sa Da Aka Kakaba Musu A Kudanci

0
316

Daga Wakilinmu

Tarar naira 100,000 ta hau kan kowacce Saniya da aka kama ta na gararanba a titi

Fulani makiyaya da ke kudancin Najeriya na kokawa kan sabbin dokoki da gwamnatin Delta ta kakaba musu da zai hanasu yawon kiwon sake.

Wannan na zuwa ne yayin da wa’adin da gwamnatin Delta ta sanya musu ke ciki, wanda ke nufin dokar da aka sanya tun a watan Satumbar bara na gab da soma aiki.

Dokar da majalisar dokokin jihar ta zartar ta ce idan aka kama makiyayi da dabbobinsa, za a ci shi tarar naira 100,000 kan duk saniya guda, da ƙarin wata 100,000 a kan mai saniyar har ma da ɗaurin shekara biyar zuwa goma.

Matakin da makiyayan ke ganin kokari ne na hana dabbobinsu sakat a sassan jihar. A wannan wata ne dai wa’adin da gwamnatin Delta ta ɗibar musu ke cika.

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen jihar Delta, Alhaji Musa Muhammad, ya shaidawa BBC cewa a kullum cikin fargaba suke game da fargabar da suke ciki.

Ya ce fatansu shi ne a nunawa gwamnan jihar dokokin da ya ke kafa musu sun yi tsauri da yawa, sannan za su kawo musu matsala tsakaninsu da masu gonaki.

”Abinda na ke nufi shi ne baki dayan jihar Delta babu wani daji, hatta gidajen da muke zaune filayen mutane ne, cikin gonaki ne da sai an zo ana cirar rogo da sauransu.

Idan aka ce za a yi lissafi, a haka Shanun da suke nan, sun fi 500,000, a zo a ce ba za mu yi kiwo ba.

Dan hakan ne muke rokon gwamna yadda mu ke zaune lafiya da masu gonaki a taimaka a bar mu haka kafin abubuwa su tabarbare,” in ji Alhaji Musa.

Ya kara da cewa daman gwamnati na kiransu da jami’an tsaro domin a yi zama, duk lokacin da aka samu wata matsala ko bullar wata fitina.

Alhaji Musa ya ce dokokin da aka kafa na cewa su tsare Shanunsu babu zuwa ko ina kiwo sun yi tsauri ga batun cin tarar Saniya da batun idan an kama su da yawa za’a biya naira 500,000.

Sannan dokar ta tanadi cewa duk wanda ya gaza biyan wanann tara zai yi zaman kason shekara 5 ko 10, ga ka ai wannan abin damuwa.”

Shugaban ya ce inda kasar arewa suke, inda akwai dazuka, da wurin shan ruwa da dukkan abin da suke bukata da sauki, amma inda suke babu dazuka ko kaura za su yi babbar matsala hakan ke zame musu.

Batun rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma kudancin Najeriya ya dade ya na ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya.

Sannan an jima ana ta kiraye-kiraye kan gwamnonin kudancin kasar su sake nazari kan haramcin kiwon sake da suka sanyawa fulanin da ke zaune a yankunansu.

Leave a Reply