Lokacin Hada Hoton Dan Takara Da Na Buhari Ya Wuce – Mahadi Shehu

0
423

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

SANANNEN dan gwagwarmayar kwato yancin al’umma da ke aikin fadakarwa da haskakawa jama’a inda aka nufa, Alhaji Mahadi Shehu ya bayyana cewa lokacin da wasu yan takara za su hada hotonsu da na Buhari da nufin su ci zabe tuni ya wuce.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wata kafar Talbijin a garin kaduna.

Mahadi Shehu ya jaddadawa jama’a cewa komai da lokacinsa don haka wancan lokacin hada hoton yan takarar neman a zabe su ya wuce kuma kamar yadda ya ce ba zai dawo ba.

“Idan ka lura mai kudin garin ku ada can shekaru Talatin amma a yanzu ba shi ba ne mai kudin, haka kuma mutum mai kyauwun siffa a garin ku a yanzu ba shi ba ne, saboda haka muke kokarin gayawa jama’a cewa komai da lokacinsa”, inji Mahadi Shehu.

Leave a Reply