Kalmar Canji Na Firgita ‘Yan Najeriya Yanzu –’Yar Takarar Shugaban Kasa

0
361

Daga: Rabo Haladu.

YAR takarar Shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar PRP, Misis Patience Ndidi Key ta bayyana cewa yaudarar wasu daga cikin ‘yan siyasar Najeriya ta sanya al’ummar kasar nan na fargaba in aka ambaci wasu kalmomi masu ma’ana mai kyau.

Key, ta bada misali da kalmar canji da jam’iyyar APC mai mulki ta yi amfani da ita wajen lashe zaben shugabancin kasa a shekarar 2015, amma sai al’ummar Najeriya suka ga akasin kalmar ta canji a aikace, sakamakon irin saba alkawari da ta zargi jam’iyyar da yi wa ‘yan Najeriya.

Key, tana ganin abinda kasar nan ta fi bukata shi ne Shugaban da ya san makamar shugabanci, wanda yake da tsarin da zai kai kasar nan zuwa tudun mun tsira, ba ‘yan siyasa masu cika baki da kurin banza ba, kamar yadda ake gani yanzu a aikace.

“Yanzu ambaton kalmar canji ma jefa wa ‘yan Najeriya fargaba da shakku yake yi, saboda yadda wasu suka yi amfani kalmar wajen yaudarar al’ummar Najeriya, alhalin ita kalmar tana da kyau sosai, don haka nake ganin abinda muka fi bukata shi ne shugaban da ya dace wajen jagorantar kasar nan, ba mai cika baki da babatun banza ba.” In ji Misis Key.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here