JIBWIS, Ba Ta Goyan Bayan Tsarin Mulkin Karba-karba A Kasar Nan

0
266

Daga; Isah Ahmed, Jos.

KUNGIYAR Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta Kasa da ke Jos, ta bayyana cewa sam, ba ta goyan bayan tsarin karba-karba da ‘yan siyasar kasar nan ke kokarin yi tsakanin Kudanci da Arewacin kasar nan.

Shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar, Sheikh Muhammad Sani Yahya ne ya bayyana haka, a lokacin da yake jawabi a wajen taron karawa juna sani na kasa, karo na 29, na kwanaki uku da kungiyar ta shirya a garin Jos.

Ya ce “zamu nunawa duk wanda yake son ya yi tsarin karba-karba damu, cewa bai isa ba, ta hanyar amfani da kuru’unmu.”

Ya yi kira ga Jama’a kan a fito ayi kuri’a domin a dakile wannan shiri na tsarin karba karba da wasu ‘yan siyasa suke kokarin kawowa.

“Jama’a gari ya waye, don haka don girman Allah muje mu yi kuri’a domin mu kare kanmu daga munafuncin tsarin karba karba, ta hanyar zabar shugabanni da zasu yi mana adalci “.

Shima a nasa jawabin, Mataimakin shugaban majalisar malamai na kungiyar reshen Jihar Yobe kuma Mai baiwa gwamnan Yobe shawara, kan harkokin addini Ustaz Babagana Malam Kyari, cewa ya yi kyakyawan shugabanci baya samuwa sai an sami shugaba mara tsoro da kwadayi wanda kuma yake tausayin, wadanda yake shugabanci.

Ya ce “duk adalcin shugaba, idan bai sami mataimaka nagari ba, ba zai sami nasara ba.”

Ya yi kira ga al’ummar Najeriya, kan su ci gaba da yin addu’o’in Allah ya zaba mana shugabanni nagari, a zabe mai zuwa na shekara ta 2023.

Hakazalika, babban bako mai jawabi kuma Sakataren gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa a Najeriya ana bukatar kyakyawan shugabanci.

Farfesa Ibrahim Abubakar, wanda Darakta Janar na bincike da adana bayanai na ofishin gwamnan Jihar Gombe, Dokta Mu’azu Shehu ya wakilta, ya ce ba za a sami tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya ba, sai an sami kyakyawan shugabanci.

Leave a Reply