NLC Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Filin Jirgin Saman Kaduna, Ta Bayyana Shi A Matsayin Cin Mutunci

0
306

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR kwadago ta Najeriya (NLC), reshen Jihar Kaduna, ta yi Allah-Wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai wa filin jirgin sama na Kaduna ranar Asabar, inda ta bayyana matakin a matsayin wani cin mutunci da zarafi ga Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban Kungiyar ta Jihar, Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, wanda ya rabawa manema labarai ranar Litinin a Kaduna.

NLC ta koka da cewa duk da yawan sojoji a yankin Igabi, ‘yan bindigar sun iya yin kutsen da suka karya ka’idojin da suka afka wajen.

“Mun tara ‘yan ta’addan da har sun hana jadawalin tashin Jirage. Wannan lamarin ya kunyata kasar Najeriya kuma dole ne kiyaye barin sake faruwar irin hakan,” in ji shi.

NLC yayin da ta yabawa hukumomin tsaro kan kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro a kasar nan, ta kuma yi kira da a kara kaimi.

Kungiyar, ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi ko mutanen da ake zargi ga jami’an tsaro da abin ya shafa don tabbatar da daukar matakin gaggawa tare da dakile hare-haren makiya zaman lafiya.

“Muna mika ta’aziyya ga ma’aikatan hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN), wadanda ‘yan ta’addan mahara suka harbe har lahira.

Leave a Reply