Gwamna Buni ya nemi ɗaukin Gwamnatin Taraiya kan ambaliyar Ruwan da ya Shafi Al’ummar Yobe

1
543

Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni, ya buƙaci agajin Gwamnatin Tarayya daga Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) domin tallafa wa yankunan al’ummomi daban-daban da ambaliyar ruwa ta shafa a yankunan ƙanana hukumomin Gulani, Gujba da sassan wasu ƙananan hukumomi a jihar.

A halin da ake ciki, Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Samarda Jin ƙai ta jihar, da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) da su kai kayan agajin gaggawa ga al’ummomin da abin ya shafa.

Gwamna Buni ya ce buƙatar hada kai da Gwamnatin Tarayya musamman ma hukumar NEMA ya zama wajibi duba da irin ɓarnar ambaliya da al’umma suka fuskanta.

A wani jawabi da Babban Diraktan Hulɗar Manema Labaru na Gwamna Alh. Mamman Mohammed ya fitar yace hukumar SEMA ta ziyarci al’ummomin da abin ya shafa domin tantance ɓarnar da aka yi, da kuma irin tallafin da ake buƙata, da kuma samar da kayayyakin agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.

READ ALSO: Buni ya nada Yusuf Ali mataimaki na musamman

Ambaliyar ta zo ne bayan kwashe sa’o’i da yawa da aka kwashe ana tafka ruwan sama a yankunan kusa da koguna.An dai yi asarar amfani gona da dabbobi sakamakon ambaliyar.

Hakazalika, kimanin rabin kilomita na hanyar da ta hada ƙananan hukumomin Gulani da Gujba ambaliya ta wanke ta inda hakan ya  katse zirga-zirga tsakanin ƙaramar hukumar Gulani daga wasu sassan jihar.

Gwamna Buni ya jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa ta hanyar  rasa gidajensu da gonaki da dabbobi, inda ya ba su tabbacin taimakon gwamnati.

1 COMMENT

Leave a Reply