Ambaliyar ruwa ta shafe gidaje da gonaki a jihar Bauchi

0
217

Daga Fatima MONJA, Abuja

Hukumar bayarda agajin gaggawa ta jihar Bauchi BASEMA, tace a kalla gidaje 100 da gonaki ne ambaliyar ta shafe a ƙaramar hukumar Darazo dake jihar Bauchi.

Muƙaddashin daraktar hukumar BESAMA, Bala Lame, ya shaida a ranar Asabar a Bauchi. Yace ambaliyan ruwan ya biyo bayan ruwan sama da akayi kwanaki uku jere kaman da bakin kwarya a yankin.

Ambaliyan ya lalata gidaje sama da100 da gonaki da dama. Daraktan ya yi jimami akan iftila’in da ya faru.

READ ALSO: Gwamna Buni ya nemi ɗaukin Gwamnatin Taraiya kan ambaliyar Ruwan da ya Shafi Al’ummar Yobe

Lame yace tuni hukumar gudanarwa ta ziyarci yankin da abin ya faru tare da tantace yawan gidajen da ambaliyar ta shafe, ya kuma ce zaa rubuta rahoto don a kawo ɗauki wa wanda abin ya shafa.

Yace ba’a samu rahoton mace-mace ko jikkata ko tacewa a ambaliyan ruwan ba. Daga ƙarshe muƙaddashin daraktan yayi gargaɗi ga mutane da su guji yin gine-gine ko zuba shara a hanyoyin ruwa.

Leave a Reply