Gonar Manja Ta Haddasa Yamutsi A Kuros Riba

0
285


Musa Muhammad  Kutama Daga , Kalaba
ASABAR ta makon jiya ce  a garin Awi da ke karamar hukumar Akampa,jihar Kuros Riba rikici ya barke tsakanin wasu manoma biyu Peace da kuma Okon har an jikkata mutum bakwai, rikicin ba a samu asarar rayukan ba.
Wakilinmu na kudanci ya samu labarin musabbanin rikicin daga bakin wani mazaunin kauyen mai suna Arith Ekpe Ndem ta ce “shi Okon dan asalin jihar Akwai Ibom ne ya dawo Awi saboda noma ya dade a nan yana gudanar da harkokinsa na noman kwakwar manja yayin da shi kuma Peace dan nan ne ba mu san yaya aka yi ba sai cacar baki ta hada su da Okon aka shiga tsakaninsu ana ganin kamar abu ya wuce ashe bai wuce ba a wurin Peace”inji shi
Ya ci gaba da cewa da yaadin ranar Asabar sai ake zargin “Peace ya gayyato wasu da ake zato ‘yan ta’ada ne suka zo kan babur goyon bibbiyu sun kai kamar babura hamsin suka afka wa kauyen nan sun sari na sara wasu kuma sun gudu gari ya watse “
Rikici tsakanin manoma a Kuros Riba ba bakon abu ba ne musamman idan hassada ta shiga tsakanin mai gona da wanda ya karbi hayar gona ya shuka amfani ya yi kyau al’amarin da bisa al’adar wuri sukan bayar da hayar gona ga mai bukata zuwa wani wa’adi idan ya girbe amfanin gonar da kaka mai gona ya karbe gonarsa.
Ya zuwa yanzu mutum bakwai da aka raunata na asibitin garin Akampa ana musu jinya.
Wakilinmu ya tuntubi DSP Irene Ugbo mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar game da lamarin ta tabbatar da afkuwar hakan duk da kura ta lafa bayan rundunar ta aike da jami’anta da ta samu labari ana sa rai ta gayyato sarakunan kauyukan ta zauna da su domin su yi bayani yaya aka yi hakan ya faru har lamarin ya kazanta.injita

Leave a Reply