Akwai Kyakkyawar Dangantaka Tsakanin KASTLEA Da NUJ Kaduna – Manjo Rimi

0
233

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SHUGABAN hukumar kiyaye hadurra ta Jihar Kaduna KASTLEA Manjo Garba Yahaya Rimi, ya bayyana cewa babban aikin da aka Dora masu alhakin yi shi ne tabbatar da tsare dokoki da dukkan ka’idojin tuki a baki dayan titunan Jihar.

Ya kara da cewa wasu daga cikin ayyukan sun hada da duba mutane masu yin amfani da wayar salula idan su na tukin mota, masu taka dokar danjar kan titi bai bayar da hannu, masu taka farin layin da ke kan tituna, kokarin kiyaye yadda kananan yara za su tsallaka Titi lokacin karatu da dai dukkan ka’idojin tukin ababen hawa kamar yadda dokar Gwamnati ta kindaya.

“Kasancewar kaduna a matsayin wata mahadar matafiya tsakanin wadansu bangarorin kasar nan dole mu tabbatar da kiyaye doka da oda musamman ga masu amfani da ababen hawa.

A cewarsa, wajen Olam ma an samu matsala tsananin jerin Gwanon motoci a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sakamakon aikin hanya a dai- dai kamfanin Olam da kan hanyar.

“A makarantu ma da suke kusa da hanyoyin da ake amfani da ababen hawa akwai jami’an mu a wajen domin tsallakawar yara yan makaranta.”

“An kuma ajiye motocin kula da marasa lafiya a wurare da dama da ke bayar da agajin gaggawa idan an samu hatsari da bai yi muni ba kafin wucewa da wanda abin ya rutsa da shi wurin kula wa da marasa lafiya na asibitoci.”

“Muna kula da masu yin gudin wuce ka’ida a cikin gari, sai kuma wata ranar da muka kama wata motar kaya bayan kayan akwai kuma mutane dari biyu da Hamsin a kan kayan duk a kan motar, dole muka kama motar da kuma kokarin hukunta Direban wannan motar.”

“Hakika muna duba lamarin manema labarai musamman idan an samu wani da ya karya dokar rashin cikakkun takardu, akwai wata ranar da muka samu wani da takardun da suka tsufa tun shekarun 1975, ko a yanzu akwai wadansu mutane yan jarida da aka tsare da batun dokar tuki suna ta kiranka, akwai kuma wata ranar da na je kafar yada labarai ta Gwamnatin tarayya Kaduna na samu wani ya ce rabonsa da canza takardu shekararsa Goma amma a yanzu ya tabbatar mun cewa zai canza takardunsa”, inji Rimi.

“Muna da kyakkyawar dangantaka da manema labarai domin sama da kashi Casa’in na yan jarida suna zuwa ko kuma kira na domin jin ta bakina a madadin hukumar KASTLEA, don haka muna da kyakkyawar dangantaka da yan jarida”.

Hakazalika, A J Suleiman, kira ya yi ga manema labarai da su rika bin ka’idar yin aikin jarida domin taimakawa al’umma da kasa baki daya

Shi kuwa, I Y Ayuba, ya yi kira ga manema labarai da su rika tantance labaran su kafin su mika shi ga jama’a, wato Ayuba ya ce su yan jarida su rika kokarin jin ta bakin kowane bangare kafin rubuta wa da aika labarai.

Jibril Abubakar Muhammad, shugaban bangaren horaswa da bincike na hukumar kula da kiyaye dokar hanya ta Jihar Kaduna, godiya ya yi ga kungiyar yan jarida ta kasa NUJ reshen Jihar kaduna da suka samu halartar hukumar KASTLEA.

Leave a Reply