‘Yan Fashin Daji Sun Mayar Da Wani Kauye A Katsina Kufe

0
272

MAFI yawan jama’ar garin Daddara na yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina, sun tsere daga garin, wasu kuma suna kwance a asibiti sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai.

Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin rasa rayukan mutum akalla biyar, ciki har da wani mai gari, kuma aka sace wasu fiye da goma.

A yanzu haka dai garin na Daddara ya zamo tamkar kufai, gashi kuma dukkan wasu al’amura na yau da kullum sun tsaya cak.

Wani da ya ziyarci garin bayan kai harin Usman Salisu Na’ikke,shugaban reshen kungiyar muryar talaka na yankin karamar hukumar Jibiya, ya shaida wa BBC cewa, ya samu mutanen da suka rage a garin cikin mawuyacin hali.

Ya ce,”Suna cikin halin tsoro da rashin tabbas, a cikin kaso uku na mutanen garin ba bu kaso biyu duk sun gudu in da wasu suka je cikin Katsina wasu kuma suka wuce Nijar”.

Dangane da batun kasancewar jami’an tsaro, Usman Salisu, ya ce ba bu wasu sabbin jami’an tsaro da aka kai garin sai wadanda dama can suke a can.

Na’ikke, ya ce maharan sun kai harin ne a daren ranar Laraba a kan ababan hawa inda wasu ke cewa sun fi dari ma mahakaran da suka je garin.

Ya ce, ” Da suka je garin sun harbe magajin garin ‘yan Gayya da dogarinsa da wasu mutum hudu, sannan sun yi awon gaba da mutum 15, amma daga baya 5 sun gudu”.

Baya ga mutanen da suka tafi da su sun kuma tafi da shanu da sauran dabbobin da suka kusan 200, in ji Na’ikke.

A na sa bangaren jami’in hulda da jama’a da rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa harin na ramuwar gayya ne maharan suka kai a garin na Daddara.

SP Gambo Isa, ya ce ” Tun bayan wani hari da barayin suka kai suka sha da kyar bayan an kashe wasu daga cikinsu, suka rinka buga waya suna cewa za su dawo don kai wani harin”.

Jami’in dan sandan ya ce jami’an tsaron da ke garin sun yi bakin kokarinsu wajen fatattakar maharan kafin daga bisani a kawo musu dauki.

SP Gambo Isa, ya ce tabbas an kashe mutum shida ciki har da mai gari, sannan kuma an ji wa wasu biyar rauni in da aka kai su asibiti.

Kazalika jami’in dan sandan ya tabbatar da sace wani shugaban riko na karamar hukumar Sabuwa a jihar ta Katsina amma kuma jami’an tsaro da suka bi barayin cikin daji sun samu nasarar ceto shi.

Ire-iren wadannan hare-hare dai na aukuwa ne a yayin da hukumomi da jami’an tsaro a Najeriya ke ci gaba da bayar da tabbaci a kan cewa suna kara himma sosai wajen kawo karshen matsalar tsaro data addabi kasar.

Leave a Reply