Jirgin Hako Man Fetur Ya Fashe A Najeriya

0
240

Daga Wakilinmu

WANI jirgin dako da hakon mai ya fashe a kudancin jihar Delta kuma ana fargabar ma’aikatan jirgin 10 sun mutu, in ji hukumomin Najeriya.WASHINGTON DC — 

Wani jami’in kamfanin hako mai na Sheba ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Ikemefuna Okafor ya ce cibiyar samar da kayayyaki ta teku da aka fi sani da Trinity Spirit ta yi aman wuta a Ukpokiti da ke gabar tekun jihar Delta a kudancin Najeriya.

Ya ce ana kyautata zaton fashewar wani abu ne ya haddasa gobarar, kuma ana kan binciken lamarin.

Ikemefuna ya ce wadanda suka fara isar da taimako kan lamarin sun hada da masunta na gida da kuma Clean Nigeria Associates, wata kungiya da ke aiki a wani wurin da ke kusa.

Ba a san adadin barnar ba. Jirgin yana iya adana ganga miliyan biyu na mai kuma fashewar ta haifar da mummunar damuwa game da muhalli.

Watanni uku da suka gabata wani malalar mai a jihar Bayelsa da ke kusa da shi ya shafe tsawon wata guda, inda ya yi barna a kasa da ruwa kafin a shawo kan shi.

Najeriya na kokarin kara yawan man da take hakowa, kuma hukumomi sun zafafa yaki da fasa bututun mai ba bisa ka’ida ba.

Jami’an man fetur sun ce kasar na asarar kusan ganga 150,000 na mai a kowace rana saboda irin wannan satar.

Leave a Reply