Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo Yasha Alwashin Kare Martabar Al’ummarsa

0
286

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba.

SHUGABAN Karamar hukumar Gwarzo yasha alwashin ci  gaba da jajircewa wajen baiwa Karamar hukumar Gwarzo tsaro -Injiniya Abdullahi Kutama

Shugaban Karamar hukumar Gwarzo, Jihar kano Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya sha alwashin ci gaba da daukar kwararan matakan tsaro a dukkan fadin Karamar hukumar domin ci gaba da Kare rayukan da dukiyar al’umma.

Karamar Hukumar Gwarzo ta kasance wacce tayi iyaka da jihar Katsina ta Yammacin kano, kana Mai Babbar hanya wacce ta hada Jihohin Katsina da zamfara kuma Babbar cibiyar kasuwanci dake yammacin Jihar.

Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya bayyana haka ga mataimakisa na musamman kan harkokin yada labarai na yan asalin karamar hukumar Gwarzo mazauna kudu maso Gabas da kudu maso kudu cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Injiniya Abdullahi Kutama wanda yake wa’adi na biyu na shugabancin wannan Karamar hukuma ya ce kasancewa Karamar hukumar Gwarzo ta yi iyaka da jahar katsina Mai makwabtaka da kano ya zame masa wajibi ya dauki matakan Kare rayukan Al’ummar Karamar hukumar da dukiyoyi su.

“Na jajirce wajen daukar matakan tsaro na ganin Iftila’in da ya shafi makwabta Jihohin Katsina da zamfara masu makwabtaka da kano bai fada wa Karamar hukumar Gwarzo ba ganin ta yi iyaka da Jahar katsina ta bangaren da Iftila’in ya fi tasiri kuma gami da Babbar hanyar da ta bi ta Gwarzo zuwa Jahohin Katsina, sakkwato, Kebbi da zamfara akwai bukatar ni da sauran Al’umma mu tashi tsaye mu bayar da gudunmuwar mu domin harkar tsaro ta tashi daga hannun jami’an tsaro ta koma tamu.”

Injiniya Bashir Kutama, har wa yau, shi ne sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumomin  Jahar kano wato (ALGON) ya ci gaba da cewa ya tanadar da duk wasu hanyoyi na samun bayanai sosai da za a ba jami’an tsaro domin daukar matakan tsaro ta yadda ‘yan ta’addar ko sun shigo Karamar hukumar ta Gwarzo ba za suyi tasiri ba.

“Alhamdulillah, mutanen Karamar hukuma ta sun fahimci mahimmancin tsaro sun tashi tsaye suna bayar da gudunmuwa sannan Ina kara masu godiya bisa dagewa da yin addu’a da suke yi akan tsaro su ci gaba dayi a kara tashi tsaye addu’a ita ce malamin”inji shi 

Kazalika ya ce yin addu’a ita ce ta fi fa’ida Allah ya rabamu da Intila’in da ya fadawa Najeriya.

Sakataren kungiyar shugabannin kungiyar kananan hukumonin kano ya kara da cewa “an kafa dokar kowa ya shiga gidan sa da zarar karfe sha daya na dare ta yi saboda baiwa jami’an tsaro dama da su da ‘yan sintiri damar samun sukunin gudanar da aikin su.”

Da ya juya kan ayyukan da zai sanya gaba musamman a wannan sabuwar shekara da muka shigo, ya bayyana wasu daga ciki ayyukan da yake da burin yi wanda suka hada da aikin bayar da ruwan sha dake Garin Getso wanda Injin Janareto ne ya rage da zai samar da wutar da zata raba ruwan sha domin aiki ne da ya lakume sama da naira milyan 360.

Sannan akwai aikin gina asibitoci guda uku idan aka tafi garin Nasarawa dake Kutama, kamar garin Harin kaura shi ma akwai aikin asibiti wanda shi ma ya yi nisa, hakazalika garin Makers, Shi ma aikin gina asibiti ya yi nisa da garin Kogin Kura, Shi ma aiki ya yi nisa “

Sannan aikwai gyare-gyaren wasu asibitoci musamman asibitin Kutama, asibitin Malamawa da garin Jama’a Shi ma ana kan aikin, kana akwai wasu asibitoci da suma aikin gyare-gyaren su yana kan gaba za su ci gaba da gina wa.

“Da yardar Allah muna kan kudurin yin haka tare da Samar da jami’an kiwon lafiya da zasu rika kula da bayar da magunguna a wadannan asibitoci wannan shi ne kudurin Karamar hukumar Gwarzo karkashin shugabanci na.”

Karshe, Injiniya Bashir Kutama, ya godewa gwamnan Jihar kano da sarkin karaye da Hakimin Gwarzo, kama daga jami’an tsaro dukkan su masu unguwanni da Dakatai na Karamar hukumar.

Leave a Reply