An Karrama Alhaji Ibrahim Kufena Da Mutane Shida

0
388

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

SAKAMAKON yabawa da aiki tukuru wajen ganin an daukaka kalmar Allah ta hanyar karantar da yara matasa Maza da Mata yasa makarantar Atiku Auwal Madarasatul Islamiyya, da ke unguwar Rimi cikin garin Kaduna ta Karrama mujahidi Alhaji Ibrahim Kufena da ke aiki ba Dare da Rana domin ganin al’amuran koyo da koyarwa sun ci gaba da inganta a makarantar.

Alhaji Ibrahim Kufena, shugaba ne a makarantar wanda ke aiwatar da aiki ba gajiyawa a koda yaushe.

Wannan ya sa aka Karrama Alhaji Ibrahim Kufena da Mutane Shida (6) wadanda a cikinsu wasu ma sun riga mu gidan gaskiya, amma duk da hakan ya sa aka ba su wannan karramawa domin yin godiya da irin abin da suka aikata lokacin da suke raye.

Wasu kuma daga cikin wadanda aka Karrama da suka hada da Maza da Mata suna nan da rayuwarsu amma an Karramasu bisa gamsuwa da aikin nasu.

An dai raba bikin saukar zuwa bangare biyu na Maza da Mata wanda a ranar farko aka fara da na saukar Maza a ranar Asabar sai kuma ranar Lahadi aka yi na Mata zalla.

Leave a Reply