Baban Gandu Zai Kawo Ci Gaba A Kananan Hukumomin Gwarzo Da Kabo – Inji Al’ummar Yankin

1
328

Daga; Jabiru A Hassan, Kano.

Al’UMMOMIN kananan hukumomin Gwarzo da Kabo sun bayyana cewa Shugaban hukumar kula da tsafta ta Jihar Kano watau “REMASAB” Alhaji Abdullahi Mu’azu Gwarzo wanda Kuma aka fi sani da Baban Gandu zai Kawo ci gaba a kananan hukumomin a matsayin ribar dimokuradiyya.

A wata tattaunawa da wakilin mu ya yi da wasu daga cikin mutanen wadannan kananan hukumomi, sun bayyana Abdullahi Muazu Gwarzo a matsayin mutumin kirki wanda kuma yake da kokarin taimakawa mutane ba tare da nuna gajiyawa ba.

Da yake karin bayani dangane da irin taimakon da Baban Gandu yake yiwa mutane kuwa, Malam Aminu Rabiu Na’abba wanda kuma shi ne daraktan Gidauniyar tallafawa ilimi ta BBNGNDU Educational Support Initiative, ya ce ko shakka babu, Alhaji Abdullahi Muazu Gwarzo zai kawo managarcin ci gaba a kananan hukumomin Gwarzo da Kabo cikin yardar Allah.

Sannan ya bayyana cewa zaben shugabanni nagari shi ne ginshikin zaman lafiya don haka yana dakyau al’umar wadannan kananan hukumomi guda biyu su duba cancanta wajen fitar da mutumin da zai yi masu wakilci Mai gamsarwa, inda Kuma ya yi fatan cewa za a jarraba Baban Gandu a kakar zabe ta 2023.

A nasa bangaren, wani matashi Mai suna Lawan Adamu daga garin Madadi ya ce yanzu haka suna yunkurin kafa babban kwamiti na tuntubar mutane domin ganin ya amsa kiran al’umma na ya tsaya takarar kujerar dan majalisar tarayya a mazabar Gwarzo da Kabo.

Sannan ya sanar da cewa Abdullahi Muazu Gwarzo shugaba ne nagari wanda kuma yake da kokarin taimakawa al’uma ta kowace fuska wanda Kuma a cewar sa, baya kyamar mutane a matsayin sa na shugaba, tare da jaddada cewa al’ummar Gwarzo da Kabo zasu rabauta sosai da romon dimokuradiyya.

A karshe, dukkanin mutanen da wakilin mu ya zanta dasu sun sanar da cewa zasu ci gaba da kokarin da suke yi wajen isar da kyawawan manufofin Baban Gandu da Kuma nuna bukatar da suke na ya amsa kiran al’umma domin ganin mutanen kananan hukumomin Gwarzo da Kabo sun Sami ribar dimokuradiyya.

1 COMMENT

Leave a Reply