Gobara ta ƙone gidan ƙaramar Ministar Abuja

0
80

Gobara ta ƙone gidan ƙaramar Ministar babban birnin tarayya, Abuja Dokta Mariya Mahmoud.

Gobarar ta tashi ne a ranar Lahadi, inda ta ƙone gidan ministar.

Gobarar ta tashi ne gidan ministar da ke yankin Asokoro da tsakar rana.

Rahotanni sun bayyana cewar jami’an kashe gobara ba su kai ɗauki a kan lokaci ba, lamarin da ya sanya gobarar yin ɓarna mai tarin yawa.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta ƙone ofishin ‘yan sanda a Kano

Duk da babu cikakken rahoto game da gobarar, amma hadimin ministar kan kafafen watsa labarai, Mista Austine Elemue, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi karin bayani ba.

Amma hadimin ya ce ana gudanar da bincike game da musababbin tashin gobarar a gidan ministar.

Leave a Reply