FCCPC za ta sake nazarin sabon ƙarin farashi akan ƙunshin tsare-tsaren Dstv Da Gotv

0
62

Hukumar FCCPC mai kare haƙƙin masu sayen kayayyaki a Najeriya tace masu ruwa da tsaki za su sake nazari akan ƙarin farashin baya-bayan nan da kamfanin Multichoice mai yaɗa shirye-shiryen talabijin ta tauraron ɗan adam ya yi, domin tabbatar da cewar bai ha’inci abokan hulɗarsa dake Najeriya ba.
A ranar Alhamis ne, Shugaban riƙon hukumar FCCPC, Adamu Abdullahi, ya yi cikakken bayani game da lamarin a shirin tashar talabijin ta Channels mai taken abuja a yau ko “Dateline Abuja” a turance.

KU KUMA KARANTA:Hukumar FCCPC ta rufe Sahad Stores

A baya-bayan nan kamfanin Multichoice, wanda jigo ne a harkar yaɗa shirye-shiryen talabijin ta kafar tauraron ɗan adam a yankin kudu da hamadar saharar Afrika kuma ke da shelkwata a ƙasar Afrika ta Kudu, ya sanarda ƙarin farashi akan ayyukan da yake gudanarwa a Najeriya, inda yace tsadar gudanar da harkokinsa a ƙasar ne ya wajabta ƙarin.

A cewar kamfanin, ƙarin farashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu mai kamawa.

Babban ƙunshin shirye-shiryen kamfanin dake kafar Dstv da a da ake biyan naira dubu 29 da 500 yanzu ya koma naira dubu 37, a yayin da ƙaramin tsarin “compact plus” da ake biyan naira dubu 19 da 800 ya koma naira dubu 25.

Leave a Reply