Fawa Ba Karamar Sana’a Ba Ce -Sarki Lawal

0
328

Musa Muhammad Kutama Daga , Kalaba

Sana’ar Fawa Sana’a ce mai  tarihi da kowace al’umma suke da masu yin ta mahauta kamar yadda aka sansu a jimlatance sun kunshi masu  fawar awaki da kuma shanu da sauran nau’ikan dabbobi .

Sarautar Fawa itama sarauta ce da take da nata sarki wato sarkin Fawa .

Aikin sarkin Fawa shi ne warware rikici Fawa,tsakanin mahauta  su ya su da kuma tsakanin mahauci da bafulatani ko ai dabba.

Domin jin yadda sarautar Fawa take a kudu, Alhaji Lawan Ibrahim  Isa sarkin Fawan Obubra kuma sarkin yakin Hausawan Kuros Riba ya yi wa wakilinmu karin bayani  domin jin yadda Fawa ta shigo Kuros Riba ,kalubalen ta da kuma yadda ma ake yin Fawar a kuros riba.Ya yi karin haske a kan haka

* Alhamdulillah wato kusan sana’ar Fawa ko shugaban cin fawa a kudancin Najeriya, ko a nan kuros riba  jihadi ne .* Kazalika ya ci gaba da cewa * Hakan yake nufi a matsaynka na shugaba ya zama wajibi ka tsaya ,ka tsare ka tabbatar cewa musamman Naman saniya Duk Inda bahaushe ya shiga  zai ci Naman saniya idan ya tambaya wane nama ne aka ce Masa Naman saniya zai Fara samun natsuwa cewa wannan Naman saniya  daga hannun musulmi ya fito suke sarrafa shi don haka zai samu natsuwa da shi fiye da kowane nama

Don haka a matsayin ka na .shugaba dole ka yi jihadin ka tabbatar da cewa duk wani nama na saniya da aka san tsarkakakke ne an yanka shi ya samu shaida cikakkiya .

Sarkin Fawan ya kkara da cewa ” Ita sana’ar Fawa kasan ita sana’a ce tun zamanin Annabawa akwai ta sannan duk inda za ka ga Fulani suna tafiya idan suka zo gari suka leka suka ga babu mahauci ba su zama garin saboda idan dabbarsu ta kasa wa zai gyara masu son haka sana’ar Fawa tana daya daga cikin dadaddiyar sana’a da ta fara shigowa kurmi “inji shi 

A cewar Alhaji  Lawan Isa ya ci gaba da cewa mahauta ‘yan asalin Arewa da suka shigo kuros riba sun isle ‘yan asalin jihar su ma na da nasu mahautan sai dai yanayin fawar ce ta banbanta da tasu “Eh ! Sun tarar da su su ma suna da nasu mahautan irin nasu maharba ,idan sun harbo naman daji su zo su kacacccala shi irin tasu fahimtar .

Amma dai Fawa ta a yanka saniya a fitar da ita dalla-dalla sai da Hausawa musulmi suka zo daga Arewacin Najeriya .sannan suka koya suka kara gogewa a harkar sannan yanayinta a yankin Obubra da ma kuros riba gaba daya wani abu ne mawuyaci saboda halin da dabba ta shiga a yanzu dabba farashin ta yayi hawan da abin malam Sai dai addu’a .saboda tsada.domin wannan dabbar babu ita a kudancin Najeriya daga Arewa ake kawo su sannan idan ka dauko ta fitinar ma’aikata ,da sauran shingayen duba ababen Hawa da ke kan hanya kafin ka iso kuros riba kudin haraji da na gyaran hanya kadai ya ishe ka don haka kafin a zo nan abin ya kure don haka kashi 90 cikin mahauta za ka gan su suna fita cikin sana’ar ba wai mayar da kudin suke yi ba .ana dai yi ne maganin kada a zauna .

Har wa yau ya bayyana dabaryn da suke yi na warware matsala tsakanin su da Fulani masu dabbobi idan sun saya dama rikicin Fawa ita kantsa tsakanin.mahautan  muna  yunkuri na yadda ake Ilmantar da su mahautan musamman a cikin.kowace sana’a jari ne mahimmin abu ne akwai tallafi da gwamnati ta cullo da su take bayarwa 

Muna duba  yiwuwar yadda a kungiyance su nemi tallafi su samu don su kara jari 

Ta fuskar Neman tallafi daga kingoyoyi ko cibiyar bayar da tallafi sarkin Fawan ya ce  Alhamdulillah akwai karamin tsari na tallafi wanda muke gudanar dashi iya daidai karfinmu ,kuma akwai shawarwari da muke ba mahauta tun daga rage yankan 

Kazalika ya bayyana irin.masarar da ya samu tun daga lokacin da ya zama shugaban kungiyar ba shi da ake biyo mahauci azo a kamashi ayi Masa wulaqanci munyi qoqarin shiga tsakiya ba za mu yadda rana daya a zo ayi wa mahauci wulakanci ba alhali kun dade kuna sana’a tare mun yi kokarin dakatar da wannan tsarin shi Bashi yadda ya shiga a hankali idan ma ya taru idan ma za’a biya shi a hankali ake yin ta sannan mun ilmantar da su mahautan su shiga tsari na zamani na taimakon juna .

Ta fuskar kubale kuwa Babban kalunalen su shi ne “Bai wuce na masu karbar rabano ba.”

Karshe ya shawarci mahautan Najeriya da na kuros riba “Kalma daya da za’a fadi ita ce a duk inda mahauci ya samu kansa ya yi taka tsan-tsan da abin da za ka saya ka yanka kasan daga hannun wa ka saya kasan hannun wanda ka saya gudun kar ka fada  kayan da ba su da kyau.”inji shi 

Leave a Reply