Farouk Mudi Na Bunkasa Kungiyar Manoma Ta AFAN – Inji Manoman Najeriya

0
325

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AN bayyana cewa shugaban hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa watau (AFAN), Alhaji Farouk Mudi na kokari wajen kyautata yanayin kungiyar a fadin wannan kasa tun lokacin da ya karbi ragamar jagorancin ta.

Wakilin mu wanda ya tattauna da wasu daga cikin manoman kasar, ya ruwaito cewa dukkanin manoman da suka zanta da Gaskiya Tafi Kwabo sun jaddada cewa yanzu kungiyar manoman Najeriya ta zamo abar alfahari wajen hada kan manoma da kokarin hada hannu da Gwamnati wajen kara inganta harkokin noma.

Alhaji Adamu Aminu Lawan, wani matashin manomi daga Jihar Kano, ya bayyana cewa yanzu kungiyar manoman Najeriya tana aiki tukuru wajen samar da yanayi mai kyau ga manoma ba tare da nuna gajiyawa ba, tare da jinjinawa Alhaji Farouk Rabiu Mudi bisa kokarin da ya ke yi na bunkasa kungiyar.

Haka kuma wata manomiya daga karamar hukumar Gumel, Hajiya Indo Garba ta nunar da cewa shugabancin Farouk Rabiu Mudi ya haifar da alheri ga manoman wannan kasa, inda ta yi kira ga kungiyar ta AFAN da ta taimaka wajen ganin manoma suna samun dukkanin wani tallafin noma da ake bukata wajen ganin ana bunkasa kasa da abinci.

Leave a Reply