Dalilai biyu da Giwaye sukafi kowane halitta dadewa ɗauke da ciki

0
400

Wani abu mai ban sha’awa da ya kamata a sani game da giwaye shi ne cewa, su ne kawai dabbobin da suka fi daɗewa da ciki a Duniya. A cewar BBC Earth, waɗannan dabbobi suna ɗaukar ciki na kimanin watanni 22, wanda yayi daidai da kimanin kwanaki 680.

Ɗaya daga cikin tambayoyin da yakamata ayi game da tsawon lokacin haihuwa na giwaye shine, me yasa wadannan dabbobin suke daukar ciki na kusan shekaru 2?

A cikin wannan labarin, za mu yi magana ne game da dalilai guda biyu da giwaye suke da dogon lokaci na ciki idan aka kwatanta da sauran dabbobi.

  1. Suna da girma matuƙa. An san giwaye a matsayin dabbobi mafi girma a duniya. A lokacin haihuwa, waɗannan dabbobin na iya yin nauyi zuwa kilogiram 91, wanda ya zarce matsakaicin nauyin jikin ɗan adam (60 kg), a cewar National Geographic.

Domin wadannan dabbobin suna da girma, har ma a lokacin haihuwa, yana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin su girma a cikin mahaifa. Girman shine ke kawo tsawon lokacin a cewar BBC Earth.

  1. Suna da kaifin basira da hankali. Yawancin bincike sun nuna cewa giwaye suna iya amfani da kayan aiki don magance wasu matsalolinsu na asali. Wadannan dabbobin na iya tara shinge don isa gun abincinsu, har ma da amfani da rassan bishiya a matsayin kayan aiki, a cewar BBC Earth.

Haka kuma an gano kwakwalwar wadannan dabbobin sun fi girman kwakwalwar dan Adam girma sau 3, kuma saboda zurfi da ƙarfin tunani da girman kwakwalwar su yana ɗaukar lokaci kafin kwakwalwarsu ta samu ci gaba, ta yadda za su dauki lokaci don ci gabansu gaba daya, a cewar BBC Earth.

Leave a Reply